Labaran Yau

Hukumar NDLEA Ta Kama Ganyen Wiwi A Jihar Legas Da Ogun

Hukumar NDLEA a ta kama Ganyen Wiwi a jihar Legas da Ogun

Hukumar kula da miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta kama ganyen tabar wiwi a garin legas da Ogun.

Mai magana da yawun Hukumar Femi Babafemi, ya bayyana hakan a garin Abuja ranar lahadi, kan cewa jami’an duruks sun kama tabar cikin wata mota Sienna, Mai Jan motan mukaila idowu an kama shi ne a gadan Otedola bridge cikin garin Ikeja jihar legas.

Ya kara da cewa an kama wani Kuma mai suna Joseph Friday ran Asabar a iyana ira a garin legas, da tabar cikin mota mai kiran Camry.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Haka kuma ranan uku ga watan mayu, jami’an sun kama wata karamar kampanin tabar wiwi skunk a safari onikolobo garin Abeokuta.

“Abinda aka karba daga wajen shi ciki akwai zobo mai wiwi cikin takai yawan kilo hudu, kwayar tramol guda dubu daya da dari takwas da tamanin da litar ruwan kwaya dari biyu da ashirin da biyar.

“Fridge Na sanyi uku, gram din tabar wiwi dari bakwai da talatin da biyar, silindar gas guda biyu da tukunya biyu” a cewar sa.

Jami’an sun kara kama mota makil da kayan maye za a tafi da ita Australia. Da kuma gidan da ake adana su a garin legas.

Kuma mai wannan gida da aka kama miyagun kwayan da wasu sabbin kayan mayen, Babafemi yake bayyana wa.

Daily Nigeria ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button