Labaran Yau

#620 Lita Guda: Yan Kasuwar Man Fetur Sun Bayyana Dalilin Tashin Farashi Da Aka Samu

N620 Lita Guda: Yan Kasuwar Man Fetur Sun Bayyana Dalilin Tashin Farashi Da Aka Samu

Shugaban IPMAN, Chinedu Okoronkwo, ya ce masu sayar da man fetur na bukatar su sayar da tsohofaffin kayan su akan sabon farashi domin samun damar ci gaba da zama cikin kasuwancin.

Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Najeriya IPMAN, ta ce nan take mambobinta suka kara farashin famfunan litar man fetur daga N500 zuwa sama da N617 a safiyar ranar Talata domin kusan dole ya zamo suyi hakan.

Shugaban IPMAN, Chinedu Okoronkwo, yayin tattaunawar sa da Channels Television a ranar Laraba.

A cewarsa, da yawa daga cikin ‘yan kungiyar ta IPMAN sun fita daga harkar kasuwanci saboda cire tallafin man fetur da gwamnati tayi saboda sun kasa samun kudin da za su yi lodi daga gidajen man fetur da kuma kamfanin man fetur na kasa (NNPC) Limited.

Okoronkwo ya ce tare da gyara farashin da hukumar NNPCPL ta yi a safiyar Talata, ‘yan kasuwa masu zaman kansu sun kara farashinsu a gidajen sayar da kayayyaki domin ya dace da tsarukan kasuwanci zamani, inda dan kasuwa zai kara farashi lokacin guda domin ya iya samun damar kawowa masu amfani da hajar tasa wasu kayan bayan wadanda suke kasa sun kare.

Duk dan kasuwa na da buƙatar kasancewa cikin kasuwanci sa. Idan ya koma sayo wasu kayan, za ku je ku saya da sabon farashi. Da a ce kana sayar da Naira 520 ne, sai an samu canji kwatsam daga inda kake samu, sai ka ci gaba da kasuwanci.” Inji shi.

“Wasu daga cikin mambobina sun kai matakin sanya kayayyaki a cikin tankunansu, kwatsam sai aka samu labarin cewa farashin ya canza. Ba su sake loda su ba. Wasu ma suna fafutuka a yanzu don ganin yadda za su yi lodin tsohon farashin da kuma sabon farashin.”

Shugaban na IPMAN ya ce ba lokacin da za a yi karin farashin ba ne, amma dole ne gwamnati ta yi aiki a kan yadda za a shawo kan matsalar daidaita farashin da kuma rage matsin farashin dala da yadda kudinmu ke chanzuwa akan dalar.

Sai dai kuma, wani tsohon shugaban kungiyar manyan ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya (PENGASSAN), Peter Esele ya caccaki shugaban kungiyar ta IPMAN.

Esele, wanda kuma ya kasance bako a shirin gidan Talabijin na Channels a ranar Larabar da ta gabata, ya ce masu sayar da man fetur na yin amfani da damar wajen samun karin riba, yana mai cewa ya dace ‘yan kasuwar su sayar da tsohon man fetur din nasu a kan tsohon farashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button