Labaran Yau

Buhari Ya Zabi Sha’aban Sharada Shugaban Hukumar Almajiranci Da Yaran Da Basu Zuwa Makaranta

Buhari ya zabi sha’aban Sharada shugaban Hukumar Almajiranci da yaran da basu zuwa Makaranta

Shugaban kasa Muhammadu buhari ya sanya hannu dan amincewa zaben Sha’aban Sharada a matsayin shugaban Hukumar ilimin Almajirai da yaran da basu zuwa Makaranta.

A cikin jawabin da yayi ranar lahadi, Garba Shehu, Mai magana da yawun shugaban kasa ya ce Buhari ya zabi sharada, dan Majalisan tarayya mai barin gado daga mazabar jihar kano. Bayan sanya hannu kan dokar kirkiro Hukumar.

“Bayan amincewar Hukumar ilimin Almajirai da yaran da basu zuwa Makaranta na 2023, shugaban kasa Muhammadu buhari ya amince da zaben dan Majalisan tarayya mai barin gado na Kano, Hon. (Dr) Sha’aban Sharada a matsayin shugaban Hukumar.

Sharada yanada digiri ta farko a fannin Mass communication daga Jami’ar Bayero ta Kano. Da Kuma digiri ta biyu MBA a jami’ar Chichester da ke burtaniya.

Thecable sun bada rahoton cewa buhari ya sanya hannu kan sabbin doka ta kasa guda uku wanda suka hada da, ofishin fansho ta majalisan tarayya, da Hukumar horaswa ta Road safety da Hukumar Almajirai da yaran da basu zuwa Makaranta.

Buhari ya mika mulki wa Bola Ahmad Tinubu ranan litinin a eagle square Abuja, bayan kammala shekaru takwas da yayi a ofishin sa na shugaban kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button