Labaran Yau

Jamb Ta Saka Sharudodin Daukan Daliban Da Suka Dawo Daga Sudan

Jamb ta saka sharudodin daukan daliban da suka dawo daga Sudan

Jamb ta bada sharudai na yanda dalibai zasu samu shiga jami’a bayan sun dawo daga kasan da ake yaki.

An bayyana hakan ne bayan jawabin Dakta Fabian Benjamin daya daga jagoran Hukumar, ya bayyana wa manema labarai a Abuja ran Laraba.

Benjamin yace sharudan an kafa su ne tsakanin ministirin Ilimi, ministirin Lafiya da Hukumar yan Najeriya na kasar waje da Hukumar jami’a na kasa.

Ya ce sun tattauna kan daliban da suka dawo daga sudan, da kuma yanda za a mayar dasu Makaranta.

Ya fadi abinda rajistaran jamb ya fadi Farfesa Ishaq Oloyede, yana da matukar amfani idan anyi magana da jagororin jami’o’i, A halin yanzu jami’un Suna bada sharudai daban daban.

Oloyede, yace sunyi zama dan su kawo sharudai da maki guda wajen daukan dalibai a jami’un daidai da sharudan daukan dalibai a Makarantun duniya.

Ya kara da cewa sanatocin jami’un zasu iya daukan dalibai da suka dawo daga sudan ba Sai sun jira Jamb ba, amma sharudan za a gindaya dan kau da korafi.

Ya bada shawara wa shugabannin jami’un da su karbi sharudai na canjin Makaranta daga kasashen waje da kuma a cikin kasa.

Yace sabuwar sharudan ba sun kau da wanda yake nan bane amma Sai dai ya karfafa wanda ya kenan din dan kawo sauki na sauyin Makaranta wa dalibai.

Daliban ya ce zasu shiga adireshin Yanan Gizo na JAMB wajen yin rajista da Kuma sanya takardun dan samun sauyin jami’a.

Daily Nigeria sun samo cewa wajen rajistan zasu saka lambar wayansu, da adireshin E Mail, Makarantar da suke, kasar da garin da suke karatun, abinda suke karantawa da Kuma ajin da suke a Makaranta.

Rajistaran Jamb ya bada shawaran jami’un da su yi kokari wajen sassauta wa daliban wajen amincewar sauyin.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button