Labaran Yau

Tinubu Ya Sanya Hannu Kan Canji Shekarar Ajiye Aiki Na Ma’aikatan Shari’a

Tinubu Ya sanya hannu kan canji shekarar ajiye aiki na Ma’aikatan Shari’a

Shugaban kasa Bola Tinubu ya sanya hanu kan sabuwar dokar ritaya na Ma’aikatan Shari’a da Kuma tsarin Fansho a kasar Gaba daya.

Yayin saka hannun, Tinubu yayi Alkawarin gyara Gudanarwan shari’a da tabbatar da shari’ar Gaskiya.

Ya kara da cewa zai yi kukarin bada guduwa wajen taimako wa Ma’aikatan Shari’a wajen saukar da nauyin da ke kansu.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Dokar ta samu amincewar Majalisan dattawa wanda ta isa hannun tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a watan mayu.

Daraktan zantarwa na fadar shugaban kasa na jiha, Abiodun Oladunjoye, yace Tinubu ya amince wa dokar.

Hakan ta nuna cewa masu shari’a a manyan kotun kasar, zasu samu karin shakara biyar na ritaya. Daga shekara 65 zuwa shekara 70.

Anyi hakan ne a daidaita shekaran ritaya na Masu shari’ar High court da sauran kotun kasa.

Hukumar labarai ta kasa tace hakan zai kara yanci da karfin gwiwa wa Ma’aikatan Shari’a.

 

Daily Nigeria ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button