Labaran YauNEWS

A Mulkina Bazan Lamunci Wani Ya Karya Doka Ba – Buhari

A Mulkina Bazan Lamunci Wani Ya Karya Doka Ba – Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga yen kasar da su guji mutanen da ke hankoron ganin sun karya doka a kasar.

Wata sanarwa da kakakin shugaban kasar Malam Garba Shehu ya aike wa manema labarai ta ambato Shugaba Buhari yana mai tabbatar wa yen kasar cewa ba zai kyale wani ya karya dokokin kasar ba.

DOWNLOAD ZIP/MP3

”Muna da kasa, muna da albarkatun kasa da kuma mutane. Sai dai ban san dalilin da ya sa wasu ke da niyyar ba da kansu ba wajen lalata ƙasarsu ba,” a cewar Buhari yayin buɗe baki da ya yi da gwamnoni da ministoci a Abuja ranar Talata.

Shugaban ya sake jaddada cewa ƙaddamar da amfani da fasahar na’urar tantance masu kaɗa ƙuri’a “ba za ta bari wani ya yi iƙirarin samun miliyoyin ƙuri’u” yayin babban zaɓe na 2023 mai zuwa.

Daga fadar shugaban kasar Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button