Labaran Yau

Buhari Ya Tura Sunayen Jiga Jigen Da Zasu Rike Hukumar Kula Da Cigaban Arewa Maso Gabas (NEDC)

Buhari ya tura sunayen Jiga jigen da zasu rike Hukumar kula da cigaban Arewa maso gabas (NEDC)

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tura wa Majalisan dattawa Sunayen Mutane goma sha biyu dan yin dan tantance su, su zama Jiga jigen Hukumar kula da cigaban Arewa ta gabas (North East Development Commission).

Shugaban kasan ya rubuta sakon nema amincewar ne wa Majalisan dattawa zuwa ga Shugaban Majalisan Ahmad Lawan ran uku ga watan mayu.

Wasikar Ta ce; “Daidai da yadda doka ta tsara na Hukumar North East Development Commission wanda aka kirkiro a shekarar 2017, Ina neman tantancewar Majalisan dattawa wajen nada jiga jigen Hukumar wanda sunayensu ke jere a kasa.

DOWNLOAD MP3

“Majalisan dattawa ta sani cewa lokacin tsofin dakarun Hukumar Cigaban Arewa ta gabas zai kare ranan 7 ga watan mayu na shekarar 2023”.

Sunayen sun hada da Barista Bashir Bukar Baale, a matsayin chairman daga Yobe, Suwaiba Idris Baba darakta babba na fannin jin kai daga Taraba, Musa Umar Yashi a matsayin darakta babba na fannnin kudi da gudanarwa daga Bauchi, Dakta Ismail Nuhu Mashka a matsayin darakta babba na fannin Aiki daga Adamawa da kuma Manajan Darakta Umar Abubakar Hashidu daga Gombe.

Wasu daga ciki sun hada da Grema Ali a matsayin mamba daga Borno, Onyeka Gospel Tony a matsayin mamba daga yankin kudu ta gabas, Mrs Hailmary Ogolo Aipoh a matsayin mamba daga yankin Kudu ta kudu, Air Comondore Babatunde Akanbi a matsayin mamba daga yankin kudu ta Yamma, Mustapha Ahmad A matsayin mamba daga yankin Arewa ta Yamma, Hadiza Maina mai wakiltar ministirin kudi a matsayin mamba daga yankin Arewa ta tsakiya.

DOWNLOAD ZIP

Shugaban kasan Yana fatan Majalisan dattawa zata duba ta tantance wanda ya tura sunayensu dan ci gaba da aikin Hukumar.

Jami’in Labaranyau ya rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button