Labaran Yau

Farashin Abinci Yana Ta Hau-Hawa A Babban Birnin…

Farashin Abinci Yana Ta Hau-Hawa A Abuja

Farashin kayan abinci ya cigaba da hawa a Abuja da jihar Nasarawa, Hukumar labarai ta kasa ta samo rahoton.

A binciken kasuwa da Hukumar labarai ta kasa tayi ranar Talata, ta bayyana cewa mutane Suna cikin tashin hankali saboda tashin farashin kayan abinci a garin Abuja da kewaye.

Daniel Chukwuekezie, Shugaban masu siyarda garin kwaki na kasuwan Masaka, jihar Nasarawa.
Buhun yellon garri Ana siyar dashi 8000 amma yanzu Ana sayar dashi 22000, nan Kuma farin garin kwaki Ana samun shi 7000 yanzu ya zama 17000.

Mista chukwuezie ya danganta tashin farashin safaran kaya. Wanda hakan ya karya karfin kundin mu.

Ezekiel Okpa wani dan kasuwa a masaka ya ce buhun wake 27,000 amma yanzu Ana saidawa 49,000.

Okpa yace buhun shinkafa ana sai da shi 15000 da 20,000 yanzu Ana siyar dashi 35,000. Sai buhun shinkafa yar gwamnati Ana siyar dashi 30000, yanzu Kuma 44,000.

Mai shagon trader a kasuwan Nyanya, Joy Peter yace lita 25 na manja 7200 bayan a baya Ana siyar wa 3,200. Lita hudu na nan gyada kuma Ana siyar dashi 5,500 yanxu Kuma 10,000 Suna nan nau’i daban daban.

Grace Ukpong tace manja da ake sayarwa 10,000 yanzu 25,000 ake siyar wa. Sai Kuma man gyada da ake siyar wa 15,500 yanzu ya dawo 32,000.

Ukpong tace abin damunta yakeyi Duk lokacin da ta je siyan kayan abinci ta. Saboda tashin farashin yayi yawa.

Abubakar Musa Mai siyar da shinkafa a kasuwan Mararaba jihar Nasarawa, yace shinkafan gida dana gwamnati Duk sun tashi, hakan yasa mutane dayawa suka koma shinkafan gida.

Musa ya bayyana cewa shinkafan gwamnati da na gida Suna 1,000 da 600 yanzu muka farashin yayi sauyi zuwa 1,500 da 900.

Janet Ibrahim, wanda ta ke sayar da masara a kasuwan Aso Pada a jihar Nasarawa, ta ce mudun masara 150 amma yanzu ya dawo 400.

Ta kara da cewa buhun masara 25,000, wanda a baya Ana siyar dashi 15,000 zuwa 10,000, nau’o’in daban daban.

Janet ta alaqanta tashin farashin da rashin shuka dawuri da Karan cin ruwan sama.

Kaminu Abubakar na kasuwan Aso Pada ta ce farashin shinkafa da wake yana tashi ne kullum saboda Damina.

“Sati biyu da suka wuce na siyar da wake 700 amma yanzu Ina siyarwa 750, saboda ruwan saman bai fadowa sosai”. Cewar ta

Motan Makinde Ola, dan kasuwan Maraba na orange market, yace farashin abinci ya karu sosai a sati biyu da suka gabata saboda tashin hankali da ke faruwa yankin kasan nan.

“Rashin tsaro da ke arewaci da Yammacin kasar yasa kayan abincin an koma kaiwa kudu maso Yammacin kasar”.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button