Labaran Yau

Boko Haram Sun Kashe Manoma 15 A Borno

An samu rahoton Yan Boko Haram sun kashe mutum goma sha biyar bayan kai farmaki a kauyuka biyu a karamar hukumar Jere na Jihar Borno.

A rahoton daily trust, yan ta’addan sun kai farmaki kauyen Kofa cikin dare sukayi ta harbe harbe ta ko ta ina, wanda sun kai har safiyan jumma’a.

An gano cewa sunyi harin a Molai kura da molai gana, sun kashe mutane da ba a San yawan su ba.

Harin da aka kai yasa mazauna wuraren sun gudu daga gidajen su zuwa cikin daji.

Wani babban dan Bijilan, Bukar Ali Musty, ya bayyana wa jaridar cewa Manoman Suna aiki a gonakinsu kusa da Molai, a wajen garin Maiduguri ranar Alhamis yayin da yan ta’addan suka kai harin suka kawo karshen rayuwansu.

“A kalla gawan mutum sha biyar aka fitar da safe, bayan harin an kai ranar Alhamis.

“Manoma bakwai aka kashe Suna aiki a gonansu, sannan aka yanka mutum takwas a gidajen su” a cewar sa.

Wasu mambobin Sibiliyan JTF sun taimaka wajen fitar da mutane daga kauyukan, bayan sun sanar da harin da aka kai. Suka ce jiga jigen jihar suyi wani abu akai dan dakile yiwuwar cigaban harin.

“Abin baiyi dadi ba kasance wa munyi kokarin dakile Duk wata hanyar farmaki a watannin da suka wuce Kuma babu hare hare a kauyukan.

“Ina wajen da safe, Ban iya tunanin cewa za a iya yanka mutane haka kamar Rago ba, duka gawakin da muka fitar Mun samesu ne jikin jini, hakan yasa dole mu tashi tsaye dan yaki da wanda basu san zaman lafiya.” Cewar mai rahoton.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button