Labaran Yau

BAM YA FASHE: Mutum Shida Sun Rigamu Gidan Gaskiya A Jihar..

Mutum Shida Sun Rigamu Gidan Gaskiya A Jihar Borno

Akalla mutum shida ne suka rasa rayukan su yayin da wasu suka jikkata bayan yan ta`adda sun harba bam mai linzami zuwa cikin garin Damboa wanda ke cikin karamar hukumar Damboa cikin Jihar Borno.

Akalla mutum shida sun rasa rayukan su ciki har da mata kuma wasu da dama sun ji ciwuka bayan fashewar bam din da `yan taadda sukayi, ya tabbata cewa yan tawayen sun je kan Gadar Waluri a garin Damboa sannan suka kaiwa yan hadin gwiwa da sojoji a wurinsu na aiki.

Daga labarin da jami`in namu ya karbo, cewa yan taaddar sun gwada dude hanyar shiga garin Damboa din amma sai basu samu nasarar hakan ba shine suka harba bam din mai linzami.

DOWNLOAD MP3

“akwai harin da aka kai garin Damboa jiya da daddare kuma mun rasa mutum shida ciki har da mata yayin da sama da mutum ashirin aka garzaya dasu asibiti, amma a halin yanzu komai anyi an gama”

Mai hada labaran namu ya karbo cewa mutanen da basu ji ba basu gani ba har mutum biyu sun samu ciwuka daga harbin bindiga.

DOWNLOAD ZIP

Da ya ke bayani jan hadarin, daya daga cikin `yan hadin gwiwar ya ce mutanen mu sun tsaya akayi fadan bindiga a nan ne ma suka harbi har mutum biyu sanna suka harba bam din suka arci na kare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button