Sakon Barka Da Sallah – Daga Hon Mubarak Haruna (Mai Rakumi)
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai
A wannan ranaku masu albarka, kuma a wannan lokaci da al’ummar Musulmi su ke cike da daukin samun rahamar Allah a matsayin sakamakon ayukkan ibada da su ka aikata a watan Ramadan, ina son in yi amfani da wannan dama domin yi mana barka da sallah.
Babu shakka a watan Ramadan da ya gabata, Musulmi sun gabatar da addu’o’i da yawa a dakin Allah (Ka’aba), da sauran wuraren ibada kamar yadda matasa da dattawa, matansu da mazansu su ka gabatar da addu’o’i a masallatai, haka kuma malamai da yawa sun yi amfani da wajajen tafsiransu su ka gabatar da addu’o’i da yawa, duka domin fatan Allah Ya kawo mana saukin rayuwa, da saukin fitintinu, Ya kuma yi wa shuwagabannin mu jagoranci, ina rokon Allah Ya amshi dukan wadan nan addu’o’i da aka yi. Da ma dukan sauran nau’ukan ibada da aka gabatar kamar ciyarwa, sadar da zumunci da sauransu.
Daga karshe, ina rokon Allah Ya zama jagoranmu a cikin dukkan lamuran mu. Ina rokon Allah Ya hana mu biyewa son zuciya, ya kare mu daga sharrin shaidan da mutanen shaidan, ya albarkaci masarautar mu ta Jama’are, jihar Bauchi dama Najeriya baki ɗaya, Ya sa dukanmu muna cikin wadanda Allah yanta.
Wassalamu Alaikum wa Rahmatullah.
Alhaji Mubarak Haruna Mai Rakumi
2 SHAWWAL 1443AH
3nd May 2022.