Labaran YauNEWS

Dalilin Ihu – Shekarau Ya Kori Dogarin Dan Sandanshi

Dalilin Ihu – Shekarau Ya Kori Dogarin Dan Sandanshi

A ranar Juma’a an hango magoya bayan Sanata Shekarau a wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta sun yi dafifi a gidan Jagoran nasu da ke unguwar Mundubawa suna yi wa gwamna Ganduje ihu da hayaniya.

Sanata Shekarau ya fusata matuka da irin halayyar da magoya bayan nasa suka aikata a jiya yiyin ziyar gwamnan, inda yace kuskure ne mutum ya zo har gidanka ka wulakanta shi ko ka yi masa rashin ladabi, ya nuna musu ba zai lamunci wannan dabi’ar ba ko da wasa.

DOWNLOAD HERE

Wata majiya da ta bukaci a sakaya sunanta ta ce, Sanatan ya tambayi ko waye yasa matasan su yi wa Ganduje ihu, sai wasu daga cikinsu suka bayar amsar cewa dogarinsa Tasi’u Dansanda ne ya saka su.

Sanatan na tunanin yi wa gwamna Ganduje ihu da kokarin rabarsa da yi masa hayaniya yayin ziyarar tasa na iya harzuka Jami’an tsaron gwamna su harbe-harbe kan mai uwa da wabi.

An ce tuni Sanata Shekarau ya kira Kwaminshinan ‘Yan sanda na Jihar Kano kan ya sauya masa shi da wani Jami’in tsaron koma waye cikin Jami’ansa.

DOWNLOAD MP3 HERE

Majiyar ta rawaito mana cewa an ta bawa Sanatan baki kan ya yi hakuri amma ya ce sam ba zai hakura ba, saboda ba tun yau ba ya sha jin maganganu daga waje wanda bai kamata su fita ba sai ya ji su a waje, kuma yasan ba wanda yake yin waya ko karbar kiran waya kusa da shi sai odilin na shi.

Har yanzu dai Sanatan na kan bakarsa na lallai sai aa sauya masa Odilinsa saboda janyo masa magana da yake da shiga hurimin da ba nasa ba a matsayinsa na Jami’in tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button