Labaran Yau

“Kar Wani Ya Raina Dan Najeriya, Dan Siyasa Tana Da Wuya Yanzu” Cewar Shugaba Buhari.

Babu hanyar Sauki zuwa Mulki – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace zaben 2023 ya nuna karfin demokradiyya a Najeriya, da kuma karfin masu zabe dan zabar wanda suke so ya nuna a fannin shugabancin.

Mai taimaka masa akan kafofin watsa labari, Shehu Garba, ya fada a Abuja ran Alhamis cewa shugaba buhari ya zanta hakan ne lokacin da Sabon sarkin Dutse ALHAJI Muhammad Sunusi ya ziyar ce shi.

Buhari yace faduwan gwamnoni goma a zaben da ya gabata dan neman kujerar sanata ya nuna cewa babu hanya meh sauki wajen cin zabe yanzu. Saboda karfin da mazabar suke dashi, yanzu meh zabe shine sarki.

“Hakan ya tabbatar da balagan demokradiyya da kuma ci gaba da aka samu wajen gudanar da zabe.
“ Tunanin kowa shine kayi gwamna na shekara takwas Sai ka tafi Majalisan dattijai ka karasa rayuwan ka.

“Kar wani ya raina dan Najeriya, dan siyasa Tana da wuya yanzu” inji shugaban kasa Buhari.

Bayan sauraron Sarkin wanda ya fadi cigaban da shugaban kasa ya kai musu da kuma neman wasu. Shugaban kasan yayi alkawarin zai yi musu abinda zai iya Kamin ya sauka akan karagar mulki.

Yayi alkawarin zai fadawa shugaban kasa Meh jiran gado Bola tinubu akan matsalarsu akan karancin ruwa a garin dutse.

Shugaban kasan yace wa shi sarkin cewa barasu manta da marigayi tsohon sarki Nuhu Sunusi ba.
Dan ya kasance aboki ne na kwarai. Kuma Suna masa addua.

Sarkin da shugaban tafiyar Muhammad Hamim sunyi godiya wa shugaba Buhari dan taimakawa wajen bunkasa noman shinkafa a jihar jigawa da kuma amincewa ayi hanyar jirgin kasa daga dutse zuwa kano.

Shugaban gargajiyan ya yaba Buhari wajen kawo zaman lafiya a Najeriya da sauran makwabtan Najeriya wanda suka jima cikin hargitsin ta’addanci.

Sarki Sunusi ya kara da jinjinawa wa buhari wajen maida sojin kasa na dutse zuwa cikakkiyar sojin burget. Da Kuma rokon shugaba buhari yayi wani abu wajen gyara matsalar rashin ruwa.

DailyNigeria ta rawaito.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button