Batun Janye Takaran Shugabancin Nigeria- Bukola Saraki
Tsohon shugaban majalisar dattawan Nijeriya Ta takwas, Dakta Bukola Saraki, ya shure wasu rahotonnin kafafen sadarwa da suka ce ya janye takarar shugaban kasa ga wani, ya ce shi sam bai janye aniyarsa na neman jagorantar Nijeriya a 2023 ga wani ba.
Saraki wanda tsohon gwamnan jihar Kwara ne, ya ce irin wadannan rahotonnin da ake yadawa da zimmar rage masa karsashin fitowa takara ba zai sanyaya masa guiwa ba, don haka ne ya nemi masu hakan ma da su canza tunani domin burinsa shi ne tabbatar da saita akalar kasar nan daga halin da take ciki a yau.
Saraki wanda ke magana ta bakin shugaban kwamitin yakin neman zabensa, Farfesa Lorwuese Hagher, ya nuna kwarin guiwarsa na cewa zai iya samun nasara a wannan kujerar ta shugaban Nijeriya.