Labaran Yau

Mawaki Davido Ya Sauke Bidiyon Daya Daura A Shafinsa Bayan Yasha Ragargaza Daga …

Mawaki Davido Ya Sauke Bidiyon Daya Daura A Shafinsa Bayan Yasha Ragargaza Daga Wurin Musulmai

Tauraron mawakin Najeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya goge faifan bidiyon wakar da yad aura a shafin sa a jiya wadda ta jawo cece-kuce, wakar wadda daya daga cikin takwarorin sa yayi, Logos Olori, bayan ya fuskanci tsangwama a yanar gizo.

A ranar Asabar, Davido ya fuskanci suka daga Musulmai da yawa a shafukan sada zumunta saboda ya yada hoton tirela mai tsawon dakika 45 na faifan bidiyo na waka a manhajar twitter.

DOWNLOAD MP3

Bidiyon wanda masu sharhin musulmi da dama suka bayyana a matsayin abin ban haushi, ya nuna wasu gungun mazaje da suke sanye da kaya, kuma ga dukkan alamu ana gudanar da addu’o’in musulmi ba zato ba tsammani ya koma rawa da waka.

Sun zargi mawakin da rashin mutunta addinin Islama ta hanyar hada ayyukansu na addini da waka da raye-raye.

Sun kuma yi kira gare shi da ya goge faifan bidiyon tare da bawa jama`a hakuri a kan lamarin.
Fitattun ‘yan Najeriya irin su Bashir Ahmad da Ali Nuhu sun yi ta tofa albarkacin bakinsu kan hakan.

DOWNLOAD ZIP

A wani sako da wani sani ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, cewa: “A matsayinka na celebrity mai nishadantarwa, idan magoya bayanka sun ji haushin wani bangare na aikinka, musamman dangane da al’adarsu, imaninsu, ko akidarsu, zai fi kyau ka goge ko gyara wannan bangaren, ka ba su hakuri, sannan ka ci gaba. Ina magana game da Davido. Wannan ra’ayi ne nawa.”

Yayin da mawakin ya yi shiru kan lamarin kuma bai bayar da uzuri a hukumance ba, kwanaki biyu bayan da aka yi masa luguden wuta, a karshe Davido ya yanke hukuncin goge bidiyon.
Wakilanmu sun tabbatar da hakan ne a safiyar ranar Litinin ta hanyar duba shafukan sada zumunta na Davido.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button