Labaran Yau

Yar Najeriya Ta Mai da Dala Dubu 80 Da Ta Tsinta

Yar Najeriya Ta Mai da Dala Dubu 80 Da Ta Tsinta Ta Damka Wa Hukumar Alhazai Na Jihar Zamfara

Yar Najeriya Ta Mai da Dala Dubu 80 Da Ta Tsinta

Mahajjaciya Aishatu Yan Guru Nahuce Yar Najeriya daga jihar zamfara, ta maida kudi dalar amurka dubu tamanin wanda ta tsunta ma Mai shi a saudiyya.

Independent hajj Reporters sun bayyana hakan a shafin su na Facebook ranan Asabar.

Shafin ta wallafa hotunan mahajjata wanda suka fito daga karamar hukumar Bungudu na Jihar Zamfara.

Sun bayyana a shafinsu cewa : “Wannan itace mahajjaciya Yar Najeriya Hajiya Aishatu yanGuru Nahuce daga karamar hukumar bungudu na Jihar Zamfara ta tsinci dala dubu tamanin wanda yakai miliyan Hamsin da shida na nairan Najeriya, ta baiwa Hukumar Alhazai na jihar zamfara domin a maida wa Mai shi, Allah ya bata ladan gaskiya ya Kuma karbi aikin ta na hajji. Aameen.”

Yabo kala kala ake tayi wa ita mahajjaciyar akan abinda tayi.

Wanda yayi magana bayan an wallafa maganar a shafin Facebook Isa Abba kyari yace “ Allah ya albarkace ta, Kuma gwamnatin jihar zamfara ta mata kyauta dan karin karfin gwiwa wa wasu su koya”.

Kayode Festus Abdulgaffar yace “Gwamnatin Najeriya ya kamata su mata girmamawa na girmamawan kasa wa wannan mutumiyar kirki in ta dawo kasa Najeriya, Allah ya biya ta.”

Sani Sulaiman Yace “Wannan abun ne Mai kyau wa kanta da iyalenta, Allah ya karbi hajjinta”

Chiri Sarki ya rubuta “Hukumar Alhazai yakamata su kyautata wa wannan mata, tayi abu Mai kyau, Kuma a bude mata akawunt dan a mata kyauta”.

Wasu sun nuna damuwa wajen zubar da kudade da mutum daya yayi masu yawa haka.

Abdullahi Muhammad Balarabe yace “Masha Allah, amma mai kudin ya dau kudaden da wuce dokar rike tsabar kudade, yakamata a bincike mai kudin a saudiyya.”

Ramalan Ahmed yace “wasu labaran basu kari, dala dubu tamanin, menene wanda yake da kudin yakeyi da kudade haka a aljihunsa a wajen aikin hajji, yana canjin kudi ne? Hmm Allah yayi mana jagora.”

A kalla mutum 95,000 suka tafi aikin hajji a kasar saudiyya wannan shekarar, Kuma an samu rahoton mutum 14 suka rasa ransu kamin aikin hajji, lokacin aikin hajji.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button