Labaran Yau

Wasu Kalamai Da Mata Keyi Wanda Maza Basu Fahimta

Wasu Kalamai Da Mata Keyi Wanda Maza Basu Fahimta 

Na fahimci babbar matsalar da maza ke fuskanta a kan zama da mata a yau shi ne rashin fahimtar yarensu… Ma’ana Lugga ko salon
da zantukansu da inda maganarsu ke fuskanta…Shi yasa yau nace zan taimakawa ‘yan uwana maza na fassara musu wadannan kalaman…gasu nan kamar haka…

-CI GABA – Wannan wani umarni ne na je-ka-ka-gani! Idan kana son zaman lafiya kada ka ci gaban…

-BA KOMAI – Idan mace ta kalli
tsabar idanunka ta ce maka “Ba komai” ka sani cewa akwai babbar magana a qasa, sai ka gaggauta neman mafita…

DOWNLOAD HERE

-WATAKILA – Idan mace ta yi amfani da wannan kalmar, To kada ka batawa kanka lokaci, tana nufin abin ba zai yiwu ba kawai…

-DA DAI A CE – Wannan ma wata
kalma ce da mata ke amfani da ita, mai harshen damo mai nufin ba a yarda da kai ba, Don haka kada ka batawa kanka lokacin yin bayanin wai dole sai ta yarda da kai…

-YA YI DAI DAI – Kana jin wannan
kalma daga bakin mace, kawai ka dauki na Annabawa – wato hakuri! Domin ba za ta kara dawowa ta kanka ba…

DOWNLOAD MP3 HERE

-KOMAI YA WUCE – Tabdijan! kana jin haka, to ka fara azumi da neman tsari daga abubuwan da za su biyo baya…Galibi wannan kalma ce da suke nufi “Bari zan yi tunanin matakin da zan dauka a kanka”…

-KANA JI NA DA KYAU ?– Malam
kada ka yarda mace ta samu galabar fada maka wannan kalmar, don haka ka rika karantar lokutan da za ka rika ba ta umarni, Idan ka kuskura ka hau nuna mata kai ne namiji ka fi ta matsayi, To a daidai lokacin ne idanunta za su rufe, ta
nuna maka cewa ba ta damu ba kuma ba za ta kara bin umarninka ba…

-ZABI NA GARE KA – Idan kana
tsamanin ta ba ka zabi ne ka yi abin da kake so to ka yi babban kuskure, Tana nufin “Ka gama tsalle-tsallenka, Amma ni na san gaskiyar abin da ya faru, kuma zan yi zabin abin da zan aikata…

-MINTI BIYAR – Idan mace ta ce
maka minti biyar, Kawai ka yi alwala ka tafi masallaci bayan ka dawo ka nemi waje ka kwanta ka ci gaba da kallon talbijin ko ka gudanar da wasu al’amuranka, domin awa daya take nufi…

-INA DA MAGANA DA KAI Abokina
ka mutu kawai…

-ME KAKE YI HAKA ? – Wannan
kalma na nuni da cewa kana yin abin da ba ta so ne, Sai ka auna yin sa da barinsa wanne ya fi mahimmanci a zamanku sannan ka yi hukunci a kai…

-ME YA SA KAKE SON KA AIKATA
WANNAN ABIN ? – Tambaya ce kuma ba tambaya ba! Tana nufin ka dakata da wannan abin da kake aikata a yanzu ka sake wani nazarin…

-YA KAMATA KA RIKA FAHIMTAR
MAGANA – Tana nufin ka rika jin
shawarwarinta…

-WANNAN ABIN ZAI MAKA KYAU – A duk sanda ka ji mace ta nuna maka abu cewa ya kamata ka mallake shi, hakika ita ce mai son abin! Tana nufin ina son
wannan abin…

-BA NA SON NA KARA YIN WANNAN ZANCEN – Idan mace ta fadi haka, tana son ka matsa a wajen, ba ta kaunar ganinka, Kwakwalwarta a lokacin tana neman
tattara bayanai ne masu hadari a kan ka…

Wadannan su ne kadan daga cikin
zantukan mata da na ci karo da su a yayin da nake gudanar da bincike na musamman game da halayensu, kamar yadda na fadi a baya… Har ila yau, idan an lura dukkan zantukan sun tafi a sabanin hakikaninsu…

Hakan ya kara tabbatar min da wani Hadisi da na karanta, wanda aka samo daga daya daga cikin jikokin Manzo Muhammad (SAW), wato Imam Muhammad Al-Bakir (as), da ya fada cewa :-

“Idan ka shawarci mace a kan abu to duk maganar da ta fada maka, ka zabi
akasin zancen, domin su gaskiyarsu a Koda yaushe, yana daidai da sabanin abin da
suka bayyana.”…

DA FATAN FASSARATA TA INGANTÀ ???

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button