Ango Yayi Shahada Domin Bada Kariya Wa Amaryarsa
Yadda Ango Ya Yi Shahada Wajen Kare Amaryarsa Daga ‘Yan Bindiga
- Sun Yi Awon Gaba Da Mata Da Yara A Garin Jere
- MazanDa Aka Kama Suka Kubuta Sun Yi Bayani Dalla-dalla
“A ranar da abin zai faru, Auwal ya kai amaryarsa Rabi’atu asibitin Unguwar Masukwani tun da safe saboda laulayin juna biyu da take da fama da shi. Da yamma bayan Isha’i dan’uwansa Rabi’u ya ziyarce shi tare da matarsa Aisha. Suka dan jima suna hira, zuwa can Rabi’u ya ce dare ya fara yi bari su tashi su koma sashinsu.
Sun tafi ba da dadewa ba, Auwal yana kwance a tabarma a tsakiyar falonsu ita kuma amaryarsa tana zaune a kujera suka ci gaba da hira, kwatsam sai ga ‘yan bindiga suka shigo musu, to dama ba su rufe kofa ba saboda dare bai yi ba sosai. Suka ce ka tashi mu tafi, ya ce babu inda zan je, sai suka ce to za mu tafi da kai da matarka ya ce babu inda za mu je, to a wannan lokacin ya mike tsaye ya tare kofar shiga falon, kawai sai suka harbe shi a hannu!
Hannun ya yi kamar an kwankwatsa da adda, ‘yar fata ce kawai take rike da shi. Suka yi yunkurin fitar da matar ya sake ce musu babu inda za ku je da ita, daga nan ne suka harbe shi a ciki, harbi uku suka yi masa. Nan take ya fadi cikin jini sai suka tafi da matar. To duk abin da ake yi akwai kaninsa Barde yana daki yana ji amma ba hali ya fita, da (Barde) ya ji (‘yan bindigar) sun fita shi ne ya fito da gudu cikin gida ya yi ihu ya ce sun kashe Danlami (Auwal).
Nan fa mutanen gida aka fiffito, to hatta lokacin da mutane suka zo duk da halin da angon yake ciki amma yana cewa ku daga ni, sun tafi da matata, ku daga ni har dai bakinsa ya rufu ya kasa magana.” Wannan shi ne takaitaccen jawabin da majiyarmu ta yi game da kisan da ‘yan bindiga suka yi wa wani ango Auwal Isah suka kuma tafi da amaryarsa Rabi’atu mai dauke da juna biyu a garin Jere da ke babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna, yankin Karamar Hukumar Kagarko a ranar Juma’a da dare.