Labaran Yau

Yan Sanda Sun Bada Belin Kwamishinan Zabe Na Adamawa

Yan sanda sun Bada belin Kwamishinan Zabe na Adamawa

Saukakken kwamishinan zabe na jihar Adamawa, Hudu Yunusa Ari, ya samu fitowa daga hannun yan sanda ta hanyar beli.

Cigaban ta samu bayan kwanaki dayayi a hanun yan sandan yayin da ya sha tambayoyi da bincike kan rashin bin doka na bayyana sakamakon zaben data gabata a jihar Adamawa.

Mai magana da yawun yan sandan, Olumuyiwa Adejobi ta tabbatar ya bayyana ranan jumma’a cewa Ari hudu ya samu beli Kuma Ana kan bincike.

Adejobi ya kara da cewa shi kwamishinan zai rinka zuwa babban ofishin yan sandan duk ranan aiki cikin sati.

Ari ya kawo jayayya bayyana Yar takarar jam’iyyar APC Sanata Aisha Binani a matsayin zababben Gwamnan Jihar Adamawa bayan ba a gama hada sakamakon zaben ba.

Hukumar zabe ta kasa ta katse sakamakon zaben Kuma ta dakatar dashi a kan matsayin sa kwamishinan zabe.

Shugaban kasa Muhammadu buhari ya bada umurnin yin bincike kan kwamishinan zaben da duka jami’an da suke tare wajen bayyana sakamakon.

Ari ya bayyana cewa baiyi nadaman bayyana sakamakon ba, domin Binani ce taci zaben Gwamna a jihar Adamawa.

Buhari ya tura sunayen Jiga jigen da zasu rike Hukumar kula da cigaban Arewa maso gabas (NEDC)

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tura wa Majalisan dattawa Sunayen Mutane goma sha biyu dan yin dan tantance su, su zama Jiga jigen Hukumar kula da cigaban Arewa ta gabas (North East Development Commission).

Shugaban kasan ya rubuta sakon nema amincewar ne wa Majalisan dattawa zuwa ga Shugaban Majalisan Ahmad Lawan ran uku ga watan mayu.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button