Labaran Yau

Yar’adua: Baramu Manta Dakai Ba Cewa Tinubu

Yar’adua: Baramu Manta Dakai Ba Cewa Tinubu

Shugaban kasa Mai Jiran gado Bola Ahmad Tinubu, Yace baramu manta da yar’adua ba.

A jawabin da ya bayyana a shafin sada zumunta, bayan Tsohon Shugaban kasan Najeriya Alhaji Musa Yar’adua ya cika shekara goma sha uku da rasuwa.

Shugaban kasa marigayi Umaru Yar’adua ya rasu ran 5 ga watan mayu a shekarar 2010.

Tinubu Ya ce:

“ Yau kamar kullum, Ina tuna abokina kuma dan uwana a hada hadan demokradiyya da mulki mai inganci a Najeriya.

Shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua ya rasu a wannan rana shekaru goma sha uku da suka wuce.

“5 ga watan mayu shekarar 2010 kamar ya jima da wucewa wa Wasu daga cikin mu, amma zafin rashin sa yana nan sabo a zukatan mu.

“Muna tuna ranar yadda muke tuna rayuwa mai inganci da yayi. A matsayin sa na aboki kuma abokin siyasa, Ina daraja shi don jajircewa da yin abu bisa tafarkin daidai da yayi wa kasa, a matsayin na gwamna a shekarar 1999 zuwa 2007, Kuma a matsayin sa na Shugaban kasan Najeriya daga 2007 zuwa 2010.

“A yayin da nake shiri dan karban karagar mulkin kasa ran 29 ga watan mayu, Ina burin koyi da Shugaban ci irin na Malam Umaru Yar’adua.

“Ya nuna cancanta da Kuma aiki wa kasa babu san kai, Allah ya jikan ka dan uwa, Allah yasa mutuwar ka hutu ne, Aameen” a cewar Bola Ahmad Tinubu.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button