Labaran Yau

Likitocin Najeriya Ta Nemi Gwamnatin Tarayya Ta Bawa Hukumar Lafiya Muhimmanci

Likitocin Najeriya ta nemi gwamnatin tarayya ta bawa Hukumar lafiya muhimmanci

Kungiyar likitocin Najeriya tace bada muhimmanci wa lafiya ake bukata dan bada kudade wajen inganta lafiya a kasa dan samun cigaba dan kar likitocin su fita aiki wasu kasashe.

Kungiyar ta fada a takardar da fitar ranan litinin, bayan taron su na 63 wanda suke zama dan tattauna wa kan lamarin lafiya, anyi conference dinne ne a garin jalingo na jihar Taraba.

Takardan ta fito da saka hannun Shugaban kungiyar Dakta Uche Ojinmah da sakatare janar Dakta Jide Onyekwelu.

DOWNLOAD ZIP/MP3

A bayanin takardan, gwamnati had gaggawa yakamata ta bawa muhimmanci kan lafiya. A kowani fanni. Kuma su nuna siyasar kula da lafiya wajen biyan albashi da wasu bukatun lafiyar kasa.

Kuma kira ne dan samar da wajen aiki mai inganci, dan kare lafiyar al’umma, a samar da tsaro dan kare lafiya da kayan mutane a asibitocin, da Kuma samar da muhalli da sauran bukatu na lokitoti a Najeriya.

Takardan Tana kiran gwamnati na kowanni matsayi suyi kokarin gyara matsalolin da daya shafi lafiya da ma’aikatan lafiya, dan kawo cigaba a wannan fanni.

“Shugaban yayi kira wa Majalisan jiha da na tarayya dasu fidda doka dan samar da yancin ma’aikatan lafiya.

“Mun bada umurni wa asibitoci su kawo hanyoyin da za’a magance badakala da rashin kula na jami’an lafiya. Dan a hukunta su da Kuma kawo gyara”.

Daily Nigeria ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button