Labaran Yau

Yan Ta’adda Sun Fitar Da Bidiyon Daliban Da Sukayi Garkuwa, Suna Bukatar Kudin Fansa Miliyan 14

Yan ta’adda sun fitar da bidiyon daliban da sukayi garkuwa, Suna bukatar kudin fansa Miliyan 14

Yan ta’addan da sukayi garkuwa da daliban kwalajin ZACAS na jihar zamfara a garin gusau. bulala yanata dukan matan yayin da suke kukan a taimaka musu.

Ummulkhairi Musa daliba ce wanda take ajin karshe da wasu mutum biyar sun fidda bidiyon matan da akayi garkuwa dasu Suna kuka a taimaka musu a daji.

Daily Nigeria ta rawaito cewa an yi garkuwa dasu a hanyan Birnin Magaji zuwa Kaura Namoda ran sha biyar ga watan junairu shekarar 2023, yayin da suke hanyar dawowa daga bakin aure.

Bidiyon ta nuna matan Suna kuka, dan Ta’adda matashi wanda ke da bindigar AK47 a rataye a wuyar sa yana zane matan da bulala.

“Da sunan Allah, ku taiamaka mana, Suna bukatar kudi miliyan naira sha hudu na kudin fansa. Iyayen mu basu da halin” a cewar su yayinda suke kuka.

Jamil Musa jami’in kwalajin ZACAS ya bayyana wa daily Nigeria cewa anyi iya bakin kokari dan asamu a karbo matan amma abu yaki kullewa.

Ya ce anyi kokari jawo gwamnatin jiha, yayin da daliban jihan sunyi kira, amma kukansu ya fada kurman kunne.

“Daya daga cikinsu daliba ta ce Ummulkhairi Musa. Ta kirani kamin su tafi bikin, cewa zata tafi bikin kawarta.

“Kuma na ja mata kunne a kan hanyar, ta ce min Allah Zai kare, Tace zata dawo lafiya amma Allah bai bari ba.

“Ta shiga hannun masu garkuwa tun watan junairu kamin a fara rubuta jarabawan su ta karshe.

“Muna kokari da yan ajinsu dan a sake ta, amma hakan bai yiwu mana ba.

“Kuma gwamnati bata dauki lamarin da muhimmanci ba, munyi dan gana ga Allah.

Iyaye da dalibai sun hada miliyan hudu an sake maza, sai hakan ya bawa mutane sanyin gwiwa kan hada kudin fansa.

Amma daga baya an sako wasu matan amma umulkhairi tana hanun yan garkuwa. Anyi magana wa mai rikon kwaryan ofishin mai magana da yawun yan sanda, Yazid Abubakar, yace Suna kokari wajen sako su.

Sunce yan Ta’addan sun gudu daga dajin zamfara zuwa dajin katsina da kaduna saboda yawan jami’an tsaro a wuraren.

“Matan an kamasu da wasu maza yayin da suke tafiya a hanyan Birnin Magaji zuwa Kaura bakida.
Yan sanda sun yi kokari a yayin da suka iya sako wasu daga ciki kamin su Bar jihar zamfara.

“Baramu hakura da neman su ba, har Sai lokacin da muka samesu” cewar Abubakar.

Daily Nigeria ta rawaito

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button