Ramadan: gwamnatin kano ta amincewa hutun sati uku wa makarantu
Gwamnatin Jihar kano ran Alhamis ta amince 7 ga watan Aprailu, A fara hutun karshen mako na biyu a makarantun gwamnati da masu zaman kansu a jihar Kano.
An samu jawabin ne daga wajen darakta Aliyu Yusuf na Hukumar ilimi na jihar ran Alhamis.
Gwamnati ta bayyana wa iyaye da waliyyai dasu yi kokarin dauko yaransu a makaranta ranar jumma’a.
Ya kara da cewa duk yan makarantan kwana Ana umurtansu dasu koma makaranta ran 30 ga watan Aprailu. Kuma sauran su koma ran 2 ga watan mayu. Ana meh Jan kunne da za a ladabtar da Duk wanda basu bi dokar komawa ba.
Dalibai da iyaye kuma Ana basu shawaran amince wa ranar komawa makaranta Kuma su kula dan kar a samu akasin haka. Fatan alkhairi wa dalibai dan yin hutu mai annashuwa.