Labaran Yau

Ku Shirya Takardar Ajiye Mukami’ Bala Muhammad Zuwa Ga Zababbun..

Ku shirya Takardar Ajiye mukami’ Bala Muhammad zuwa ga zababbun masu mukami

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad ya bada umurni wa duk masu mukaman siyasa da su shirya takarda sake karagar mulki, Kamin 29 ga watan mayu lokacin da za rantsar dashi.

Kauran Bauchi ya bada umurnin ne a yayin da aka kafa kwamitin canza gudanar wa na gwamnati a gidan gwamnatin Bauchi ran laraba.

“A yanda kuka sani, tenuwar mu ta biyu zata fara ne ran 29 ga watan mayu, 2023. Lokacin za a rantsar dani na biyu a madadin shugaba na wani shekaru hudu wanda zai kawo karshen wannan tenuwa.

DOWNLOAD MP3

“Haka kuma Duk zababbun masu muqamin siyasa zasu ajiye domin mu kawo sabbi.

“Kuma baramu yi kasa a guyiwa ba don dawo da wanda suka yi aiki tukuru” A cewar sa.

Gwamnan ya jaddada amfanin takardan canza muqamin, zaiyi amfani wajen taimakawa sabbin kwamishinonin da zasu karbi karagar mulki don yin aikin da ya kamata.

DOWNLOAD ZIP

Bala ya tabbatar da cewa hakan zaiyi amfani ne ba don canza gwamnati ba, Amman saboda fahimtar aikin da akayi don gyara da yin abinda yakamata dan cigaba.

Ya kara da cewar Kamin karshen shekaru hudu na sabon tenuwansa ta kare, zai tabbatar da jihar bauchi tayi gasa da kowata jiha a kasar Najeriya.

Mambobi daga kowani karamar hukuma za a zaba don yin adalci kuma shugaban kwamitin shine Arc. Audu Katagum, sakataren kuma Alhaji Samaila Burga.

Gwamnan ya bayyana sauran mambobin zasu bayyana bada jimawa ba.

Kuma duka kwamishinonin da ciyamomin kananan hukumomin Suna cikin kwamitin.

Daily nigeria ta rawaito.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button