Karamar ministar harkokin ‘yan sanda, Imaan Sulaiman Ibrahim ta bukaci matasan Najeriya da kar su yi zanga-zangar da za a yi a fadin kasar a ranakun 1-10 ga watan Agusta.
Imaan Sulaiman-Ibrahim, ta bada tabbacin cewa ma’aikatar harkokin ‘yan sanda ta dukufa wajen daukar matasa 30,000 aikin ‘yan sanda.
Ta jaddada cewa shugaban kasa Bola Tinubu yana da kyakykyawan aniya ga ‘yan Najeriya kuma ya jajirce wajen magance kalubalen tattalin arzikin kasar.
Imaan ta ce ma’aikatar ta kuma fara daukar matasa 10,000 aikin ‘yan sanda a shekara ta 2024. Ta ce ma’aikatar ta inganta kokarin magance cin zarafin ‘yan kasa da wasu jami’ai ke yi.
Ta kara da cewa jindadin jami’an ‘yan sanda ya dauki matakin ne a ma’aikatar. Ta bayyana cewa zanga-zangar ba za ta magance yunwa da kalubalen da ‘yan kasar ke fuskanta ba.