Daga Gwamnati, fadar shugaban kasar ta yi ikirarin cewa wadannan kungiyoyi suna adawa da manufofin ci gaba na shugaba Tinubu da kuma mayar da hankali kan sanya matasa cikin harkokin mulki.
Sunday Asefon, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan hada-hadar dalibai, ya bayyana hakan a yayin wani taron majalisar gari game da shirin gudanar da zanga-zangar, wanda Mista Osahon Okunbo, shugaban Wells Carlton Hotel and Apartments ya shirya a ranar Laraba, 31 ga watan Yuli a Abuja.
A wani lamari makamancin haka, Legit.ng ta ruwaito cewa, fadar shugaban kasar ta yi zargin cewa wasu ‘yan daba da makiya Najeriya ne ke shirya zanga-zangar da aka shirya don samun daman cinma muyagun manufofinsu.
Samun yin hakan agaresu na iya kawo tsaiko cikin inganta alakar gwamnati da matasa. Tashin hankali bashine mafita ba.
Gwamnati ta jima tana kin goyon bayan zanga-zangar, duk da cewa ‘yan kasa nada iko da damar yin hakan a dokance indai ta kasance ta lumanar ne.
Babban sufetan ‘Yan sanda,