Labaran Yau

Nasan Ana Wahala A Najeriya Amma Don Allah Kar Ku Yi Zanga-Zanga – Wike Ya Roki ‘Yan Najeriya

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya yi kira ga mazauna Abuja da kada su shiga zanga-zangar da ake shirin yi a fadin kasar.

Wike ya yi wannan roko ne a lokacin da yake zantawa da mazauna Abuja bayan ya duba aikin da ake yi na hanyar da ta isa Saburi 1 da 2 mai tsawon kilomita 5 a karamar hukumar Abuja Municipal Area, AMAC, a Abuja ranar Alhamis.

Wasu ‘yan Najeriya da ba a san ko su waye ba sun shirya gudanar da zanga-zangar lumana kan yunwa da rashin tsaro a kasar daga ranar 1 ga watan Agusta.

Sai dai ministan ya ce shugaba Bola Tinubu na sane da damuwar ‘yan Najeriya kuma yana iya bakin kokarinsa wajen ganin cewa ya magance matsalolin cikin gaggawa.

A jawabin shi yake cewa yunwa da wahala a halin yanzu wani yanayi ne na wucin gadi.

Ministan ya ce nan ba da jimawa ba sauye-sauye da manufofin da ake yi za su samar da sakamakon mai kyau da ake bukata.

Ya yi zargin cewa wasu ‘yan siyasa ne ke shirya zanga-zangar da nufin kawo cikas ga gwamnatin Tinubu.

Ministan Sadarwa ya fito yayi jawabi kan cewa Shugaba Bola Tinubu na kokarin fara bawa matasan da suka gama Jami’oi da kolejin kere kere alawus kowani wata.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button