Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta bayyana Abubuwa uku Wanda zata gabatar a ranar zabe.
Jami’inmu na Labaranyau Blog yasamo rahoto kan cewa INEC za ta gudanar da ayyuka uku a cibiyar da suka hada da sanarwar wadanda suka yi nasara, gabatar da takardar shaidar cin zabe ga zababben shugaban kasa da mataimakinsa; da kuma zababbun Sanatoci da ‘yan majalisar wakilai.
Ya bayyana cewa ‘yan takarar shugaban kasa da suka hada da Bola Tinubu na jam’iyyar All Progressives Congress APC; Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP; Peter Obi na jam’iyyar Labour Party LP, da sauran su za su rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta karshe a ranar Laraba 22 ga watan Fabrairu.
Yakubu ya kuma bayar da tabbacin cewa karancin Naira a halin yanzu ba zai haifar da barazana ga gudanar da zaben ba saboda hukumar ta samu kwakkwarar tabbaci daga babban bankin Najeriya CBN cewa za a samar wa ita hukumar INEC da kudaden da ake bukata.
Yakubu wanda ya samu rakiyar kwamishinoni na kasa da kuma wasu manyan jami’an hukumar ta INEC tun a baya ya kai ziyarar duba horar da jami’an sa ido na SPO na zaben a makarantar sakandiren gwamnati da ke Garki a Abuja.
Ferfesa Yakubu Yakara Da Cewa;
“Kamar yadda kuka sani, mun yanke namu aikin a fili sannan wasu kuma an yanke nasu ayyukan a boye amma abu mafi muhimmanci shi ne muna aiki tare kuma jami’an tsaro sun tabbatar mana da cewa za su tabbatar da ingancin zabe a fadin kasar nan. . Don haka ba mu da wata matsala ta wannan fuskar.