Labaran YauNEWS

Rasha Ta Aiko Da Muhimmin Saqo Ga Daliban Nijeria Ta Kuma Basu Guraben Karatu

Rasha Ta Aiko Da Muhimmin Saqo Ga Daliban Nijeria Ta Kuma Basu Guraben Karatu

 

Kasar rasha tace a shirye take don bada dukkan wani tallafi da gurbi na karatu ga dukan daliban nijeriya dake bukata.

Kasar  Rasha ta kuma ce za ta cigaba da bada duk wanu taimakon da ya dace domin tabbatar da tsaro da walwalar yan Najeriya da ke Rasha.

Mikhail Bogdanov, mataimakin ministan harkokin kasashen waje na Rasha,  ya fitar da sanarwa tare da bada tabbacin yayin wani taro da Abdullahi Shehu, jakadar Najeriya a kasar.

Bogdanov, wanda ya tarbi jakadan na Najeriya a ofishinsa, ya tabbatarwa Shehu cewa Rasha za ta bada taimakon da ya dace don tabbatar da tsaro da walwalar daliban Najeriya mazauna Rasha.

 

Hakan na zuwa ne yayin da rikici ya barke tsakanin Rasha da Ukraine da ya yi sanadin mutane da dama suna tserewa daga Ukraine.

Ya kara da bawa jakadan Najeriyan tabbacin cewa Rasha ta dauki Najeriya a matsayin kasa mai muhimmanci a Africa kuma za ta cigaba da karfafa dankon zumunci da ita.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button