Labaran Yau

Tinubu Ya Zabi Ribadu, Alake, Edun Da Wasu Mutum 5 a Matsayin Masu Shawara

Tinubu Ya Zabi Ribadu, Alake, Edun Da Wasu Mutum 5 a Matsayin Masu Shawara

Shugaban kasa Bola Tinubu ya zabi tsohon shugaban Hukumar EFCC Nuhu Ribadu, a matsayin mai bada shawara na tsaro da kuma tsohon kwamishinan Zantarwa Dele Alake, a matsayin mai bada shawara wa Shugaban kasa kan Zantarwa da tsare tsare.

A bayanin da daraktan Zantarwa na fadar shugaban kasa na jiha, Abiodun Oladunjoye yace shugaban kasa ya bawa Yau Darazo Mai Bada shawara kan Siyasa da gwamnatin Cikin gida. Wale Edun Kuma yazamo mai bada shawara akan Dokikin kudade.

Bayanin ya kunshi cewa, Tinubu ya amince da zaben Olu Verheijen, a matsayin mai bada shawari kan Energy da kuma Zachaeus Adedeji a matsayin mai bada shawara akan Haraji.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Wanda suka samu sa hannun shugaban kasa sun hada John Ugochukwu Uwajumogu a Mai bada shawara kan Kampani, kasuwanci da hannun jari da kuma dakta Salma Ibrahim Anas Mai bada shawara akan lafiya.

Daily Nigeria ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button