Gwamnan Kano Ya Dawo Da Daukan Nauyi A fannin Ilimi
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana dawowar Daukan Nauyin Ilimi (scholarship) wa masu wanda suka samu 1st Class bayan kammala Jami’a wanda suke so suyi karin karatu na gaba a kasar Najeriya ko kasashen waje.
Gwamnan Jihar, Abba Yusuf Kabir yace hakan yazo ne da cika alkwarin da yayi lokacin takarar gwamna dan gudanar da kudirin sa na tsarin Ilimi.
A bayanin Da yafito ta wajen sakataren zantarwa, yace gwamna a amince wa sakataren gwamnatin jiha da fara bada Scholarship na fita kasar waje wa yan kano wanda suka gama Jami’a da 1st Class.
“In an tuna, scholarship ta karshe anyi ta ne karkashin mulkin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a shekarar 2015 wanda ya dau nauyin masu 1st class 503 zuwa kasashen duniya 14 a fadin duniya” cewar sa.
Bayanin ta bayyana cewa, Ana gayyatan wanda suka cancanta daga jihar kano Kuma suke so su kara karatun gaba ta masters a kasashen waje a daukan nauyin 2023/2024.
“Duk wanda ya cancanta Kuma yana so a dauyin sa, Sai yazama cikakken dan jihar Kano da Kuma 1st class daga Jami’an gwamnati ta Sani, da Kuma lafiyan iya fita kasar waje dan karatu.
“Wanda ya cancanta Kuma yake da Duk abinda ake Nema. Zai iya garzayawa wannan website www.Kanostategov.ng./scholarship dan cikawa Kuma za a gayyaci wanda suka cika a ofishin sakataren gwamnatin jiha dan Tantancewa. Ana bukatan su halarci ofishin da takardun su kamar haka:
Takardar shaidan dan kasa, takardan lafiya, takardan haihuwa, takardan gama Firamare, takardan kammala jami’a, takardan Waec ko NECO. Za a kammala nan da kwana sha hudu daga ranar Jumma’a.” Jawabin ta bayyana.