Labaran Yau

Tinubu Ya Samu Goyon Bayan Gwamnonin kan Cire tallafi

Tinubu Ya Samu Goyon Bayan Gwamnonin kan Cire tallafi

Shugaban kasa Bola Tinubu ran laraba ya amshi goyon baya akan kudirin kawo karshen tallafi mai a kasar da wasu dokoki na sabon mulki.

Shugaban kasan ya karbi goyon bayan ne bayan ya gayyaci mambobin kungiyar gwamnonin Najeriya, da jagoran cin ciyaman dinsu Abdulrahman Abdulrazak na kwara a fadar jiha na shugaban kasa a Abuja.

Gwamnonin sun bayyana jin dadinsu kan cire tallafi daga jagorori da sauran manyan kasa.

Sun taya Shugaban kasa murna wajen kawo maslaha kan cire tallafi, da alkawarin kawo sauki na matsalar da zata iya aukuwa na karamin lokaci kan hunkuncin.

Tinubu yayi kira ga Gwamnonin su bada hadin kai wa Gwamnatin Tarayya wajen kawo sauki wa mutane da suke cikin talauci a fadin kasar, Yace yanayin da mutane suke ciki abun dubawa ne.

Shugaban kasan ya bada shawara wa shugabannin siyasa su ajiye siyasa da banbanci dan aiki wajen kawo karshen wahala da mutane ke ciki.

“Matsayin mu na kau da talauci, ya kori siyasa, Mun zo ne dan Najeriya da Kuma gina kasa.

Tinubu ya bayyana cewa yakamata mu kalli kanmu a matsayin babban iyali guda daya.

“Mun zama iyali daya a gida daya, Muna kwana a dakuna daban daban. In mun kalli abun ta wannan idon, Zamu cire mutanen mu a halin talauci.” Inji shi.

Shugaban kasan yace mulki na adalci zai kare kudirin demokradiya.

“Yanzu haka a nan, Mun taru ne a daki Kuma daga qabilu daban daban, amma mu kasa daya ne. Hadin kai da zaman lafiya, ya rataya ne a wuyan mu.

“Mun yi kokarin kula da kanmu ta hanyar demokradiyya, munyi campaign Kuma Mun samu kanmu a wannan wuri, dole muyi aiki wa mutane.”
Ya bada shawara da gwamnoni.

Tinubu ya musu Alkawarin cewa zai bar kofar sa a bude ma wanda yake da wani ra’ayi na cigaba ma kowa.

“Muna bukatan hadin kai dan yaki da rashawa, Muna kokarin yaki da masu shigo da haramtaccen kaya. Kuma mu hada kan mu dan gyara tattalin arzikin kasa.

“Bayan cire tallafi, akwai kudade da Zamu Tara a Asusun kasa” Inji shi.

Tinubu yace fannin ilimi ya kamata a bunkasa dan korin talauci da laifuffuka.

Ya yi tuni kan rashin zaman lafiya a wasu jihohi kuma ya ja kunne wa gwamnoni wajen dakile duk wasu matsala.

Abdulrazak ya ce sunyi alkawari wa shugaban kasa akan gwamnoni zasu bada goyon baya wa Gwamnatin Tarayya.

Daily Nigeria ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button