PoliticsLabaran Yau

Ganawar Kwankwaso Da Majalisar Tarayyar Turai EU, Da Jakadun Nahiyar Turawa

Kwankwaso ya gana da majalisar Tarayyar Turai EU, da Jakadun Nahiyar turawa mutun Ashirin da biyar 25

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria People’s Party NNPP, Sen. Rabi’u Musa Kwankwaso, PhD, FNSE, da mataimakinsa dan takarar shugaban kasa Bishop Isaac Idahosa sun gana da shugabar tawagar Tarayyar Turai a Najeriya, Ms Samuela Isopi tare da Jakadun kasashe mambobin EU 25 a Sakatariyar Tarayyar Turai, Abuja.

Taron dai ya baiwa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP da masu masaukinsa damar tattaunawa kan batutuwan da suka shafi moriyar juna tsakanin Najeriya da kasashen kungiyar EU.

DOWNLOAD ZIP/MP3

kwankwaso ya kuma yi amfani da hanyar wajen gabatar da Tsarinsa Kundin manufofin sa ga Jakadun Tarayyar Turai. An tattauna batutuwa da dama a taron.

Cikin wadanda suka raka dan takarar shugaban kasa wajen taron akwai Engr. Buba Galadima, Barista Ladipo Johnson, Dr. Baffa Bichi, Hon. Garba Ibrahim Diso, da Abdulmuminu Jibrin Kofa.

Sauran bayani cikin hoto

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button