Labaran Yau

Hukumar Kwastom Ta Kano Da Jigawa Ta Samu Naira Biliyan ….

Hukumar kwastom Ta Kano Da Jigawa Ta Samu Naira Biliyan 18.8 A Wata Shida

Area command ta Kano-Jigawa na Hukumar kwastom na kasa ta karbi kudaden harajin karya doka sama da Naira biliyan Goma sha takwas da digo takwas. Daga junairu zuwa watan Yuni.

Area Kwanturola Sambo Dangaladima, ya bayyana hakan a tattaunawar sa da manema labarai a kano ranan laraba.

DOWNLOAD MP3

Yace “Mun saka jami’an mu a wuraren zasu iya magance mana matsaloli na shigo da haramtattun kaya da kuma kasuwancin da baya kan tsarin doka”.

Shugaban kwastom din ya bada oda wa jami’un su da su zauna a kan bodar dan magance matsalar shigowa da abubuwan da kasa ta hana.

“Munyi shirin yakin kawo karshen wannan matsaloli na safaran kaya” Cewar sa.

DOWNLOAD ZIP

Dangadima ya nemi goyon bayan shugabannin Al’ada da masu fada a ji wajen jawo hankalin mutane kan matsalar safaran kaya da kuma illar ta wa kasa baki daya.

“Munyi magana da samarin kauyukan bodojin mu dan taimakawa jami’un mu da bayanin da zai taimaka wa wajen dakile safaran kaya. Command din ba wurin zuwan masu safaran kaya bane” ya ce.

Ya kara neman goyon bayan masu fada aji wajen magana da mazauna garuruwan da su guji safaran kaya, su bi dokan shigowa da kaya da fitar wa.

Dangadima ya yi Jan kunne wa masu safaran kaya da da masu taimakawa da su nisanta har kan a gaba.

NAN

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button