Labaran Yau

Ku Zabi PDP Daga Sama Har Kasa – Sakon Kauran Bauchi Ga Ningawa

Ku Zabi PDP Daga Sama Har Kasa Za Mu Cire Kitse A Wuta – Sakon Gwamna Bala Ga Ningawa

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Abdulƙadir Muhammad yayi kira ga masu kaɗa ƙuri’a da su zaɓi ƴan takara ƙarƙashin inuwar jam’iyyar PDP don cigaba da sharɓar romon dimokraɗiyya, inganta zaman lafiya da tattalin arzikin jihar Bauchi da Najeriya.

Bala Muhammad na jawabi ne a garin Ningi yayin gangamin yaƙin neman zaɓe a madadin ɗan takarar shugabancin Najeriya Alhaji Atiku Abubakar da dukkanin ƴan takara a kujeru daban daban.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Ga Sakon Gwamna Bala Kauran Bauchi Zuwaga Ningawa

Gwamna Bala ya faɗawa Ningawan shirin gwamnatin sa na cigaba da kyautata rayuwa da samar da sauyi ta hanyar yaƙar talauci, inganta harkar noma, kiwon lafiya da sufuri kana yace ayyukan da gwamnatin sa ta kammala a zargo farko a ƙaramar hukumar sun haɗa da gyara da samar da turakun lantarki, kwaskwarima wa fadoji, gina rukunin gidaje masu rangwame da sauran su.

Yace jam’iyyar PDP ce ɗaya tilo dake kare muradin Najeriya da ƴaƴanta ba tare da haddasa ƙabilanci addini, yanki ko ƙabila ba, a saboda haka ya kirayi al’uma da su ƙauracewa zaɓar gura-gurbin ƴan siyasar da yayi wa laƙabi da ungulu da kan zabo.

Gwamna Bala ya ƙara da cewa gwamnatin sa ce ta farko a tarihin jihar Bauchi da ta bada matasa da mata damar shiga a dama da su kai tsaye cikin hidimar mulki, kasuwanci, siyasa da horaswa kan noma da kiwo don gina goben su.

Photos Below;

Reporter: Lawal Muazu Bauchi
Me tallafawa Gwamna Bala kan kafafen yaɗa labarai na zamani
Janairu 24, 2023.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button