Labaran Yau

UNICEF Da NPC Zasuyi Rajistan Haihuwa Wa Yara Guda Miliyan..

UNICEF da NPC zasuyi rajistan haihuwa wa yara miliyan 1 a Kano

Majalisan dinkin duniya karkashin kudin yara da Hukumar kidaya ta kasa, zasuyi rajistan haihuwa ta miliyan daya wa yara a kano a shekarar 2023 ta hanyar na’urar Zamani.

A zaman nasu ta kwana biyu, jiga jigen sukayi kan rajistan haihuwa ta na’ura ran Alhamis. Shugaban ofishin UNICEF ta kano Rahama Farah, tace a kalla yara Miliyan daya zatayi wa rajista a shekarar 2023.

Wanda ya wakilce ta Micheal Banda, ya cewa Rahama tace yancin dan kasa doka ce ta kare rayuwan dan kasa. Kuma ya bayyana cewa hakan yana daga cikin muhimmin yanci na kowa.

DOWNLOAD ZIP/MP3

“Kasashe daban daban nuna muhimmancin yan kasa da yancinsu ta hanyar rajistan haihuwa. Wanda hakan kuwa ya sanya kare yara daga haihuwansu” a cewar sa.

A bayanin shi bincike ta nuna a yara hudu da aka haifa yaro daya bayi samun rajistar haihuwa a Najeriya. Mafi yawan wanda ke kasa da shekara biyar.

“Binciken MICS 2021 ta nuna cewa yaran da aka musu rajistan sun kai kashi 33 cikin kaso dari wanda duk suna da shaidar haihuwa”

Farah ta bayyana cewa UNICEF Tana taimaka wa Gwamnatin Najeriya ta Hukumar kidaya dan samo hanyoyin da za a samu yin rajistan haihuwa wa yaran da aka haifa.

Ya yi murna wa gwamnatin jihar kano na yin rajistan haihuwa kashi 55 cikin kaso dari Kuma da aiki tukuru dan samun cigaba da Kuma kokari wajen karasa kashi 45 na wanda basu samu rajista ba.

Daily Nigeria ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button