Gwamnan Jihar Bauchi ya Halarci bikin daurin auren dan mataimakin sa
Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Muhammed ya halarci bikin daurin auren dan mataimakin sa, an daura auren Muhammad Baba Tela da Fatima Saminu Abdurrahman ran Asabar sha uku ga watan mayu a garin Azare.
Wanda suka halarci daurin aurena babban masallacin Azare sun hada da jiga jigen yan jam’iyyar PDP da sauransu.
A wurin taron daurin auren, Bala ya musu addua da Kuma yin koyi da Al’ada, girmama juna da fahimta, kuma sune idon ahalin su, suyi kokari suyi abinda ya dace a zamantakewa.
Bayan nan shi gwamna ya kara halartan bikin fatima Audu SULE katagum wanda ta auri Abubakar Sadik.
Mohammed ya ce Allah ya basu zaman lafiya da kuma zuri’a dayyiba.
Lawal Mu’azu, Mai taimakon gwamna a fannin zantarwa na shafin sadarwa ya bayyana hakan.