Ruwa A Jallo Nake Neman Mijin Aure – Fidausi Ismail
Wata Budurwa mai suna furdausi Ismail ta nuna bukatar ta a fili game Neman mijin aure Budurwar wacce ta rubuta a shafinta na sada zumuntar zamani na Twitter ta rubuta ne acikin kalmar yaren turanci tana mai cewa (I NEED A HUSBAND) ma’ana tana bukatar mijin aure.
Lamarin da yaja hankalin tare da cece kuce daga wasu masu bibiyar shafin Budurwa wasu na ganin wannan Budurwa ta nuna rashin kunya Kasancewar ‘yan mata masu kunya musamman musilmai basu fiye fitowa karara domin nuna bukatar su ta aure a idon jama’a ba.
A wannan wata na Azumi ‘yan mata da dama na yawan nuna bukatar su ga neman mijin aure.