Labaran Yau

Mahmood Yakubu Yayi Aiki A Karkashina Kamin Ya Zama Shugaban Hukumar Zabe

Mahmood Yakubu yayi aiki a karkashina kamin ya zama shugaban Hukumar zabe

Dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaben da ta gabata Peter Obi, yace Mahmud Yakubu chairman na Hukumar zabe ta kasa INEC, yayi aiki a karkashin sa.

Ya fadi haka ranar jumma’a a jihar Anambra, a wajen bikin wallafa littafin sa Peter Obi: Murya dayawa, Alkibla daya (Peter Obi “Many voices, One Perspective”).

“ Shekara ta uku a kotu a jihar Anambra Ina neman karbo kujera ta ta gwamna, dan ban aminta da lamarin ba. Mutane sun yi kokarin hanani, amma nace musu ko shekara hudun zai kare zai nayi gyara Zan samu gamsuwa da cikan buri.
“Abinda nake fada akai shine Muyi abinda shine daidai, Ina fadawa kowa ni baran bawa kowa kudi yayi abinda bai dace ba. Na jagoranci kwamitin TETFUND wanda Farfesa Mahmud mamba ne a kwamitin, mun san juna, bayan ya zama shugaban Zabe, Bamu hadu ba, kuma na fada mishi cewa shi Mai gani da zantarwa ne, kayi abinda ya zama daidai.

“In ka samu dama kayi abinda yafi daidai, inka bari akayi rashin daidai, hakan zai shafemu gaba daya, Ina maimaitawa muyi komai daidai” cewar Obi.

Tun zaman tinubu Shugaban kasa, tsohon gwamnan anambra yaki ya karbi kaddarar fadi zaben shugaban kasa yake ta korafi da kara a kotun Abuja.

Daily trust ta rawaito

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button