EntertainmentLabaran Yau

Asalin Saurayinda Ya Juyawa Rakiya Moussa Poussi Baya Ya Bayyana

Asalin Wanda Ya juyawa Rukaiya Mousa baya a soyayya ya bayyana

Kamar yanda labarin Rakiya Mousa ya riskemu jarumar dai yar kasar nijar ce wanda ta shahara a kannywood wajen yin fina finan hausa, waka da rawa.

Jaruman ta kasance mawakiya wanda ta bayyana cewa ta gada ne wajen mahaifinta wanda shima ya shahara wajen yin waka da hausa da yaren nasu na kasar nijar a shekarun baya.

Malama Rakiya ta sanu a bidiyon wakokin mawaka kamar su Hamisu Breaker, Auta Mg boy da sauransu.

DOWNLOAD MP3

Rakiya Musa Da Hamisu Breaker
Rakiya Musa Da Hamisu Breaker

Shekaran jiya Hadiza Gabon tayi posting bidiyon tattaunawar ta da Rakiya Mousa, a yayin da ita Gabon ta mata tambaya akan koh an cuce ta koh ita ta cuce wani a soyayya. Wanda jaruman ta ce ita bata cuta sai dai a cuce ta.

Ta kara da bayyana cewa Tana soyayya ne da mutum in har Tana sonsa. A cikin tattaunawarsu, rakiya ta fashe da kuka take bayanin cewa shi wanda takeso ya yanke alaqa da ita.

Rakiya Musa Poussi
Rakiya Musa Poussi

Kuma tayi iya kokarinta dan ta cire shi a ranta abu ya gagara. Tace Suna tare ne tun kamin ya sanu a duniyar waka.

DOWNLOAD ZIP

Hadiza Gabon ta kara da tambayanta akan in ya dawo yau zata aure shi? Ta bayyana cewa tabar wannan ga Allah, amma barata iya auren wani ba saboda har yanzu Tana sonshi Kuma har ta mutu barata daina ba.

Maza dayawa suna neman aurenta amma ta rasa yanda zatayi ta auri mutum Tana tunanin wani.

Hasali ma tace zata aureshi koh da baida hanu koh kafa koh da yana tiri tiri akan titi.

Labarinta ya kasance meh ban tausayi da mamaki wanda ya karada yanan gizo. Har mutane suna zargin mawaki Hamisu breaker shi ya bata hot breakfast a fadin wasu.

Mutane Da yawa sun karkata kan hamisu breaker wanda suka fi alaqanta wanda ya yaudareta breaker ne.

A wani peji a fesbuk meh suna Uncle Comrade, ya bayyana cewa shahararren mawakin Hamisu breaker ya fito yayi magana.

Bayan tsawon lokaci da aka dauka ana zargin cewa da shi jarumar take a yayin hira da abokiyar aikinta Hadiza Gabon ta yi da ita, saidai Mawakin ya fito ya wanke kansa kamar haka;

“Assalamu alaikum masoyana tare da fatan kun sha ruwa lafiya, dazu wasu daga cikin masoyana suka ja hankali akan wannan batun da yake ta yawo cewa Rukayya Yusuf ƴar asalin Niger wadda Hadiza Aliyu tayi hira da ita, wasu mutane na cewa wai da ni ta yi soyayya kuma har na juya mata baya.

Sam-sam wanna maganar ba haka take ba, hasali ma ni babu wata alaƙar soyayya tsakanin mu sai dai mutunci”.

A kwana a tashi, a sannu gaskiyar

Asalin Saurayinda Ya Juyawa Rakiya Moussa Poussi Baya Ya Bayyana
Asalin Saurayinda Ya Juyawa Rakiya Moussa Poussi Baya Ya Bayyana

maganan da wanda ya mata hakan zai bayyana.

Ku kasance tare da Labaranyau.com don karin bayani.

Kalli Hiran Hadiza Gabon Da Rakiya Musa Poussi Inda Tayi Bayani Akan Rayuwar Soyayyarta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button