Buhari ya siya Jiragen sojojin ruwa 20 a shekara takwas cewar Shugaban sojin ruwa
Sojojin ruwan Najeriya ta ce jiragen ruwa Guda Ashirin aka siyo wa sojin ruwan Najeriya, a shekara takwas karkashin mulkin Shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Shugaban dokoki da tsare tsare na babban ofishin sojin ruwa Rear Adm. Saidu Garba, ya fadi hakan a tardar da ya saka hannu ran jumma’a.
A bayanin Garba, yace an siyo jirage daban daban kamar su Offshore patrol vessel, Landing ship transport, seaward defense Boats, kananan jiragen sama, da kuma kananan jiragen ruwa na sintiri tsaro.
Ya ce a sakamakon gudumawar da buhari ya bayar na cigaban sojin ruwan Najeriya a karkashin mulkin sa, yasa zamu bashi kidayan abubuwan da ya kawo mana dan girmamawa.
Taron zasuyi ne mai taken “Cigaban kasa” national prosperity wanda za ayi a legas ran 19 zuwa 22 ga watan mayu.
Shugaban sojin ruwan ya kara da cewa Shugaban kasa ya bude jirage biyu da aka kera a kasar Najeriya, daya a shekarar 2016 da kuma shekarar 2021, ya Kuma sa ayi wasu jiragen guda biyu wanda zasu kammalu a shekarar 2024.
Taron PFR ta shekarar 2023 za ayi ne dan karrama Shugaban kasa Buhari, dan aiki da yayi tukuru dan karfafa kasa da yayi.
Garba yace anyi bikin na karshe a shekarar 2010, a mulkin Goodluck Jonathan da Kuma bikin jika shekara 50 da Najeriya ta samu yanci.
Ya kuma kara da cewa Najeriya taje bitan jiragen ruwa na wasu kasa da tutarsu a jiragen. A jirgin ruwan Najeriya Aradu.
“Mun tura sojojin mu bitan jiragen ruwa Bangladesh a watar disamba na 2022. Bikin murnan zagoyar samun yanci” a cewar sa.
“Wasu kasashe masu jiragen yaki zasu hallara dan bitar jirage da za ayi kasar Najeriya. Spain, Brazil da ghana Suna daga ciki”
Garba ya nuna cewa mulkin buhari ya kawo kyakkyawan cigaba a fannin sojin ruwa na kasa.
Yace hakan ya nuna zuciyar siyasa da yasa dan aiwatar da ayyukan da ya ce.
“Bitar jiragen ruwa da za ayi ya kasance bikin cigaban da Buhari ya kawo da karfafa kasar wajen nuna karfin da sojin ruwan suka samu dan cigaban Najeriya” cewar Garba.
Daily Nigeria ta rawaito