Labaran Yau

Hukuncin Satar Man Fetur Ba Zai Zama Sassauka Ba

Hukuncin Satar Man Fetur Ba Zai Zama Sassauka Ba

A kwanakin baya ne dai aka ruwaito cewa Kamfanin Mai na Nigeria National Petroleum Company Limited, da wani kamfani mai zaman kansa mai suna Tanita Security Services, a wani samame na hadin gwiwa sun kama wani jirgin ruwa dauke da danyen mai a cikin jirgin.

A wata sanarwa da babban jami’in sadarwa na kamfanin NNPC, Garba Deen Muhammad ya fitar, jirgin mai suna MT TURA mai lamba ta International Maritime Organisation mai lamba 6620462 mallakin wani kamfani mai rijista a Najeriya mai suna HOLAB MARITIME SERVICES LIMITED mai lamba RC813311 ya nufi kasar Kamaru dauke da kaya a lokacin da aka kama shi a ranar 7 ga watan Yuli.

Kamfanin NNPCL ya ci gaba da cewa, sakamakon binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa an sace danyen da ke cikin jirgin ne daga wata rijiyar mai da ke gabar teku a jihar Ondo.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Ga al’ummar da ta shafe shekaru da dama tana fama da rahotannin satar danyen mai ta hanyar ruwa, matakai za`a dauka nag aske.

Sai dai yawan satar da ake magana a kai, kimanin tan metric ton 150,000, da kuma lalatar da jirgin ruwa da danyen mai ya haifar da damuwa a tsakanin ‘yan Najeriya.

Majalisar wakilai a zamanta ta yi kira ga jami’an tsaro da su daina kona jiragen ruwa da aka kama da ke dauke da satar man fetur domin kada a ta’azzara matsalar gurbatar muhalli a yankunan da ake hako mai a Najeriya.

A yayin gabatar da kudirin da Hon. Thomas Ereyitomi kan batun, majalisar ta yanke shawarar bincikar lalata jirgin da kuma abin da ya faru da danyen fetur din da aka sace cikin jirgin
Ereyitomi ya bayyana cewa, wannan ba shi ne karon farko da hukumomin tsaro ke gudanar da irin wannan aika-aikar ba wanda ke da illa sosai, musamman ga rayuwar al’ummar yankin.

Ya kara da cewa, a watan Oktoban shekarar da ta gabata, an kama wani jirgin ruwa mai suna MT DEIMA wanda ke dauke da metric ton 1,500 na danyen sata a kogin Escravos, inda ya yi nuni da cewa irin wadannan ayyuka idan aka bar su su ci gaba “zai kara shafar rayuwa da walwalar ‘yan Neja Delta wadanda ke da kamun kifi a matsayin babban sana’arsu.

Amma da yake kare matakin, daraktan na NNPCL ya ce bayanan kamawa da binciken jirgin an mika su ga hukumomin gwamnati da suka dace, inda aka ba da umarnin a lalata jirgin, “domin ba tun yanzu jami`an ke samun rahotanni akan jirgin ba.

Kamfanin NNPCL ya karkare sanarwar da cewa, “Sana`ar satar danyen man fetur ba bisa ka’ida ba, ba wai kawai yana jawo babbar asarar tattalin arziki ga Najeriya da masu ruwa da tsaki a harkar man fetur ba, har ma da ci gaba da cin hanci da rashawa, lalata muhalli, da kuma rashin zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Hukumar ta NNPCL ta ce babu daga kafa ga duk wani jirgi da aka kara kamawa da danyen fetur din haka nan zaa saka sojoji su lalata shi ta hanyar wullo masa bamabamai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button