“Siyasar Kano Sai Kano” – wannan kirari ne na siyasar Kano da ke jan hankali a arewacin Najeriya.
Yana da matuqar wahala a ce siyasar kowani gari ta zama iri ɗaya, a kan samu bambanci lokaci zuwa lokaci daga wuri zuwa wuri a fadin kasan.
Ko wane lokaci yakan tafi daidai da yanayi na tirihin siyasar Kano, musamman idan an buga gangar siyasa a Najeriya.
A tattaunawar da BBC tayi da masanin siyasa a Najeriya mai suna Dr Kabiru Sufi wanda ya yi bayani kan abubuwa biyar da suka shafi siyasar Kano.
Masanin Siyasar ya ce akwai abubuwan da suka sa ake yi wa siyasar Kano kirarin “Siyasar Kano sai Kano” wanda har ya sa ta banbamta kuma take jan hankali – waɗanda ya bayyana kamar haka:
An Chanza Ranakun Da Za’a Gudanarda Zaben Fidda Gwani (Primary Election) Na Jam’iyyar Apc
Ga Dalilai Biyar Da Yasa Siyasar Kano Yafi Jan Hankali A Nijeriya
1. Tarihi
Tarihin siyasar Kano yadda aka fara da yadda aka yi gwagwarmayar siyasa ya tasirantu ne kan al’ummar jihar.
Shi tarihin siyarsan Kano ya samo asali ne daga gwagwarmayar siyasar da aka yi kafin samun ƴancin kai musamman bayan ƙirkirar yankin arewa da aka yi a shekarar 1946, da kuma kafa siyasar farko ta NPC da aka yi a yankin a 1949 da kuma kafa jam’iyyar NEPU a 1950.
2. Yawan al’umma
Kano jiha ce mai yawan al’umma a Najeriya, kuma ɗaya daga cikin jihohin da ke tasiri a siyasar Najeriya.
Yawan al’umma wanda ke tasiri ga yawan ƙuri’a ne ke sa ake sa ido a siyasar Kano.
3. Sauyin da siyasa ta samu
Zuwan kafofin sada zumunta na intanet da yawaitar kafafen yaɗa labarai sun ƙara haifar da sauyin siyasa a Kano.
An samu wayewar kai sosai saboda wanzuwar kafafen yaɗa labarai na zamani da kafofin sada zumunta – zuwansu da ƙaruwarsu ya sa yanayin siyasar ya sauya.
4. Rarrabuwar kai
Tun bayan jamhuriyya ta ɗaya zuwa jamhuriyya ta biyu kamar rikicin da aka samu a jam’iyyar PRP ya sa a cikin jam’iyya ɗaya za a samu rarrabuwar kai a samu gidajen siyasa sun rarrabu.
5. Rashin tabbas
Yanayin siyasar Kano ya sa ba za a iya ci mata alwashi ba.
Tarihi ya nuna babu tabbas a yanayin siyasar Kano. Abubuwa na iya sauyawa, haka ma lisaffi da alƙalumman yanayin siyasar na iya canzawa cikin ƙanƙanin lokaci.