Labaran YauNEWS

Daga Karshe Anyi Jana’izar Mutane 100 Da Mahara Suka Kashe A Filato

Daga Karshe Anyi Jana’izar Mutane 100 Da Mahara Suka Kashe A Filato

An Yi Jana’izar mutanen da hare-haren ‘yan bindiga ya shafa a kauyuka 4 dake Karamar Hukumar Dangi, mahara ne suka kashe fiye da mutum 100 a harin da suka kai ranar Lahadi da safe a jihar Filato.

Mutanen yankin sun tattara gawarwarki sama da 100 bayan hari inda suka yi wa mafi yawansu jana’izar bai daya. Har zuwa lokacin hada wannan rahoton hukumomin jihar da na ‘yan sanda ba su kai ga ayyana takamammen adadin wadanda yan bindigar suka kashe ba.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Da misalin karfe daya na ranar Talata ne ‘yan bindigar suka dira kauyukan Kukawa da Gyanbahu da Dungur da kuma Keram, inda suka dinga kashe mutane ba gaira ba dalili, yayin da suka raunata mutane masu dama, tare da cinna wa gidaje wuta, da kona antena-antena na kamfanonin sadarwa.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan Sanda ASP Ubah Gabriel ya ce; zuwa yanzu ban tabbatar da adadin wadanda aka kashe ba, ko adadin gidajen da aka kona ba, amma da zarar mun gama tattara rahotonmu za mu sanar sa manema labarai.

Shugaban Karamar Dangi da lamarin ya faru, Alhaji Dayyabu Garga ya tabbatar da cewa mutanen da aka kashe sun wuce 100, don shi da kanshi ya zagaya kauyukan da lamarin ya faru, ya kuma bayyana cewa wannan shine hari na farko irinshi a Karamar Hukumar ta Dangi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button