Labaran Yau

Mutum Uku Sun Rasu Sakamakon Hadarin Mota A Hanyar Lagos Zuwa….

Mutum Uku Sun Rasu Sakamakon Hadarin Mota A Hanyar Lagos Zuwa Ibadan

Har mutum uku ne suka rasa rayukan su sakamakon hadarin mota da ya auku a kan hanyar Lagos zuwa Ibadan ranar Jumua. hadarin ya ratsa da Mota kirar Toyota Sienna..

Motar Toyota Sienna mai dauke da Lambar Mota BDG 426 HT da kuma Motar DAF mai dauke da lamba RNG 558 XC.

Labari ya iso daya daga cikin jami’in Labaranyau Blog cewa motar Sienna din ce ta daki motar DAF din a yayin da take fitowa daga garejin.

DOWNLOAD MP3

Mai magana da yawun hukumar Kiyaye Hadarurruka ta Kasa, shiyyar Jihar Ogun Florence Okpe shi ya shaida wa Jami`in mu jim kadan bayan aukuwar hadarin ta wayar salulala, wannan shi ya bada tabbacin aukuwar abun.

Mai magana da yawun hukumar ya bayyana mana cewa hadarin ya auku ne a daf da gidan man Total kan hanyar Lagos Ibadan din.

Jami`in ya kara da cewa a nan take mutum bakwai suka ce ga garin ku nan wanda ya hada da matasa Maza guda hudu, Mata guda biyu da kuma yaro guda daya ne hadarin ya shafa.
Okpe ya kara da cewa gudu da motar sienna din ta keyi a kan hanyar babu kakkautawa shi ne babbar sila.

DOWNLOAD ZIP

Wadanda suka samu raunuka kuwa nan take aka garzaya da su Babban asibitin da ke garin domin agaji na gaggawa sannan kuma wadanda suka rasa rayukan nasu aka kai nasu gawawwakin Mutuware a karamar hukumar Ipara.

Maikata na nan gurin hadarin suna kula da yanayin wurin. Jagororin hukumar kiyaye hadarurruka sun nemi matuka da su dinga tafiya ta hankali a ko ina suka tsinci kansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button