Labaran YauNEWSTrending Updates

Ina Goyon Bayan Matasa Su Fita Zanga-zanga – Senata Abdul Ningi

Azaman gaggawa da majlisar dattawa tayi, Senata Abdul Ahmed ya goyi bayan matasa akan suyi zanga-zangar amma cikin lumana

A ranar laraba, 31 ga watan Yuli ne majalisar dattawa tayi zaman gaggawa dan shwon kan matasa batu barin yin zanga-zangar 1 ga watan agusta.

A bayanin Senata Abdul Ahmed Ningi, senata me wakiltan bauchi ta kudu, ya nuna cikakken goyon bayansa wa matasa akan fita zanga-zangar ta lumana da za’ayi daga 1 zuwa 10 ga watan Agusta.

Abdul Ningi yace tunda gwamnatin tarayya ta kasa daukan mataki, guntu ko dogo akan matsalar yunwa da ke ratsa cikin kasa, yana mika goyon bayanshi kan zanga-zangar.

Majalisar dattawan ta yi zaman gaggawan ne a babban birnin tarayya Abuja, domin yunkurin nemo mafita wa kasa kan zanga-zangar lumanan.

Hakan ya jawo kace nace sosai daga manyan senatoti wurin nuna damuwan su da tausayawa wa ‘yan kasa bisa yunwar da ake ciki.

Senata Abdul Ningi, ya nuna damuwan sa ga talakawa ga irin tsadar abinci ke kara karuwar a kasuwannin kasan. Sannan ya ja kunnen matasa kaman haka

“Babu Taba Kayan Kowa, Babu Kona Kayan Kowa, Ayi ZANGA ZANGA Cikin Limana.”

A watannin da suka gabata, senata Abdul Ningi ya samu hutun dole daga majlisar dattawa na kasa bisa ga sukan da yakawo kan bojet din kasa da aka sake.

Ya kalubalanci majalisar dattawa da ta sake duba wannan bojet bill din ganin akwai kuskure a ciki. Yin hakan ya jawo kace nace tsakanin senatoti daga zone daban daban.

Har aka kai da Dakatar dashi daga halartan zaman dattawan na wasu lokaci, aka kuma bukaci ya kai takardan hakuri. Jajir cewan shi akan damuwan talakawa bai tsaya a nan ba ya kai ga goyon bayan zanga-zanga dan a samu mafita.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button