Girke GirkeLabaran Yau

Yadda Ake Gwaten Dankali (Irish Potato Pottage)

Yadda Ake Gwaten Dankali (Irish Potato Pottage)

Ita Paten dankin turawa abinci ne da ake yi da ci a fadin kasar Najeriya da wasu kasashen waje amma an fi yin shi a Jos, saboda Ana noman shi mafi yawa a garin Jos da Jihar Filato (plateau).

Kayan hadi
Dankali kamar na 500naira
Nama na 500naira
Bushasshen kifi na 300naira
Ginger (citta) 50naira
Tafarnuwa (garlic) 30naira
Manja ko Mangyada gwangwani 1
Attaruhu na 50naira
Tattasai Na 100naira
Albasa Na 50naira
Maggi guda 8
Gishiri kadan
Ganye na 100naira
Karas (carrot) na 100naira
Onga classic guda daya

DOWNLOAD ZIP/MP3

Yadda Ake Hadawa

Dafarko zaa wanke nama a zuba cikin tukunya a daura kan wuta, asa citta da tafarnuwa da albasa Maggie da gishiri abarshi ya fara dahuwa idan yadau dahuwa sai a wanke bushasshen kifi asa su dahu tare sai a juye a kwano

Sai a fere dankali a yanka su kar suyi Manya kar suyi kanana daidai asa ruwa Dan kadan da gishiri idan ya tafasa sai a juye nama da kifin da ruwan Naman Akai asa manja da markadadden attaruhu da tattasai da albasa asa Maggie da gishiri a barshi ya dahu sai a zuba ganye a rufe idan komi ya hada kanshi ganyen ma ya nuna sai a sauke.

Gwaten Dankali
Gwaten Dankali

Idan Kuma za a saka karas (carrot) to Mangyada za a saka saboda yafi Dadi ba manja ba.

Ganyen zaa iya Saka kowane ya danganta da wanda akeso.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button