Majalisan tarayya ta kira Ministan Al’amuran waje kan lamarin Sudan
Majalisan tarayya ta nemi ministan Al’amuran waje, da Hukumar kula da harkokin waje(NIDCOM), da Hukumar tallafi na Annoba NEMA da su zo dan yin bayani kan matsayan lamarin fitar yan Najeriya a Sudan.
Shugaban Majalisan tarayya Femi gbajabiamila ya fadi wajen taron Majalisan akan tashin hankali da fitan yan Najeriya daga Sudan.
Gbajabiamila Yace, a satin da ta gabata, kasar Sudan sun shiga wanda yasa mazauna kasar Najeriya a Sudan cikin rudani.
Yace, don haka Ana ta kokari dan fitar da yan Najeriya, mazauna, dalibai, ko wani abun daban sukeyi a kasar.
An samu matsaloli dan rashin tsari dake cikin hukumomin da suke alaqa da fitar yan Najeriya.
Hakan kawo matsaloli wajen fitar dasu.
“Mu Kuma anan muna kokarin kawo sauki da tallafi wa dan kasa, yakamata mu duba matsayan da ake ciki na lamarin dawowar dan fahimtar ingancin aikin”.
Ya kara da cewa yakin da akeyi a sudan tunatar da Majalisan kan lamarin rabewa dan haka kar mu cire idon mu kan Gaskiya.
A bayanin shi yace a tashin hankalin mun fadi, amma cikin zaman lafiya, kowa yaci gaba.
Kuma da rashin gaskiya, da san zuciya, basu baiwa zaman lafiya, hadin kai wurin zama ba.
“Idan munki Gaskiya, Toh Mun fadi kuma munji kunya a idon tarihi” a cewar sa
Daily Nigeria ta rawaito