Labaran YauNEWS

Dalilan Tsige Limamin Masallacin Apo, Sheikh Nuru Khalid

Dalilan Tsige Limamin Masallacin Apo, Sheikh Nuru Khalid

Kwamitin gudanarwar masallacin Juma’a na rukunin gidajen ‘yan majalisu da ke unguwar Apo a birnin tarayya Abuja, ya dauki matakin dakatar da babban Limamin masallacin, Sheikh Nurudden Khalid, bisa caccakar shugaban kasa, Muhammadu Buhari a mimbarin huduba kan harin da ‘yan bindiga suka kai wa jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ranar Litinin din da ta gabata.
Limamin a cikin khudubarsa da ya gabatar ranar Juma’a, ya soki shugaba Buhari kan kin zuwa Kaduna domin yin jaje kan harin da ‘yan ta’addan suka kai, da nuna ko oho da sauran matsalolin tsaro da suka addabi kasarnan, Limamini ya yi tir da irin wannan lamarin.
Ya nuna cewa Buhari ya je Kaduna domin kamfen amma ya ki ya taka kafarsa zuwa jihar bayan da harin Bom ya rutsa da fasinjoji a cikin jirgin kasan.
Shugaban kwamitin masallacin, Sanata Sa’idu Dansadau, ya bayyana cewar an kori malamin ne bisa gabatar da huduba ta tunzurawa da tayar da zaune-tsaye a ranar Juma’a 1 ga watan Afrilun 2022.
Sanatan ya ce, koyarwar malamin ya saba wa tsarin addini, don haka suka dauki matakin dakatar da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button