A jiya ne kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta yi barazanar fara yajin aikin sai baba-ta-gani a fadin kasar nan daga ranar 14 ga watan Agusta, idan har a karshen aiki a ranar Juma’a 11 ga watan Agusta ba a janye tuhumar da gwamnatin tarayya ke yi mata ba.
A taronta na majalisar zartarwa ta kasa, NEC, taron na nazari kan zanga-zangar da aka gudanar a fadin kasar a ranar Laraba, NLC ta bukaci a janye tuhumar da ake yi mata na raini cikin gaggawa.
Sanarwar da aka fitar a karshen taron, ta ce shugabannin NLC sun kuma bayar da dalilan dakatar da zanga-zangar da aka gudanar a fadin kasar, tare da bayyana cewa mambobin hukumar sun yi nazari sosai kan halin da al’ummar kasar ke ciki, a cikin wahalhalu da rashi da ake fama da shi a dukkan jihohin kasar nan.
Kamar yadda sanarwar ta bayyana, NEC ta kuma yi nazari kan tasirin zanga-zangar a fadin kasar, musamman ganawar da suka yi da shugaban kasa Bola Tinubu, da shugabannin majalisar dokokin kasar da kuma matakin raini da gwamnatin tarayya ta dauka ta hannun kotun masana’antu ta kasa, NICN.
‘’ Domin tabbatar da ranar 19 ga Agusta, 2023, inda za a amince da batun karin farashin man fetur, bisa la’akari da tabbacin shugaban kasa da majalisar dokokin kasar.
‘’Domin shiga yajin aikin gama-gari a fadin kasar nan.
“Don fara yajin aikin gama gari daga ranar Litinin, 14 ga watan Agusta idan har gwamnatin bata janye wannan sammacin na kotu ba.